karamar Hukumar Koko-Besse za ta gina kasuwa ta naira miliyan 435

karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi za ta kashe Naira miliyan 435 domin gina sabuwar kasuwa ta zamani a garin Koko.Shugaban karamar hukumar Alhaji Buhari Aliyu danmasanin Koko ne ya bayyana haka a lokacin da yake zagayawa da ’yan jarida domin gane wa idonsu yadda aikin kasuwar ke gudana. Shugaban ya ce kasuwar an […]

karamar Hukumar Koko-Besse za ta gina kasuwa ta naira miliyan 435
karamar Hukumar Koko-Besse za ta gina kasuwa ta naira miliyan 435

karamar Hukumar Koko-Besse da ke Jihar Kebbi za ta kashe Naira miliyan 435 domin gina sabuwar kasuwa ta zamani a garin Koko.
Shugaban karamar hukumar Alhaji Buhari Aliyu danmasanin Koko ne ya bayyana haka a lokacin da yake zagayawa da ’yan jarida domin gane wa idonsu yadda aikin kasuwar ke gudana.
Shugaban ya ce kasuwar an bada kwangilarta ne saboda kasuwar da ake ciki yanzu ta yi cushe inda a ranar Juma’a da take ci ake samun cinkoson jama’a da abubuwan hawa. Ya ce jama’ar karamar hukumar yawancinsu manoma ne don haka ya zama wajibi a samar musu wadataccen fili da shagona domin ajiye amfanin gonarsu idan sun kawo kasuwar.
Alhaji Buhari Aliyu ya ce kasuwar za ta dauki shago 500, kuma za a ware wa kowane bangaren kasuwanci bangarensa, kuma akwai karamin asibiti da ofishin ’yan sanda da na ’yan banga.
Ya ce “Kasuwar ita ce ta biyar tun lokacin da aka kafa garin Koko, ta farko ita ce Kasuwar Marina sai Kasuwar Gari da Kasuwar Daji da Kasuwar Turaku, wannan ita ce ta biyar da muka sanya wa suna Kasuwar dan-gindi (International Model Market).
Alhaji Buhari ya ce ci gaban da ake samu da bunkasar tattalin ariziki a karamar hukumar ne ya zama wajibi dole a samu babban wurin da za a gina kasuwa ta zamani, kuma kamfanin da ke wannan kwagila wato Hydro Company Ltd ya yi alkawarin zai kamala aikin kasuwar a cikin wata uku zuwa hudu.