Karamar Hukumar Lere na cikin matsalar rashin kudi – Shugaba

Shugaban karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya ce karamar hukumar tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin kudin da take fama da shi. Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da ya yi da hakiman yankin a garin Saminaka. […]

Karamar Hukumar Lere na cikin matsalar rashin kudi – Shugaba
Karamar Hukumar Lere na cikin matsalar rashin kudi – Shugaba

Shugaban karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya ce karamar hukumar tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon rashin kudin da take fama da shi. Alhaji Ibrahim Abdulkarim Lazuru ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro da ya yi da hakiman yankin a garin Saminaka. Ya ce, “Magana ta gaskiya muna cikin wani mawuyacin hali kan rashin kudi a wannan karamar hukuma, kudin da ake turo wa karamar Hukumar Lere daga Asusun Tarayya ba Gwamna ne yake rikewa ba, yanayin halin da muka tsinci kanmu a ciki ne ya sanya muka shiga cikin wannan matsala.” Alhaji Ibrahim Lazuru ya ce baki dayan kudin da muke samu daga Asusun Tarayya a duk wata, ba sa wuce Naira miliyan 180. Ya ce a cikin wadannan kudi ne a duk wata suke biyan albashin malaman makarantun firamare na Naira miliyan 106, suke biyan albashin ma’aikatan karamar hukumar Naira miliyan 57, kuma ana cire kudin ’yan fansho sama da Naira miliyan 20 da kuma kudin da ake shirya wa ma’aikata tarurrukan horarwa da sauransu. Ya ce “Don haka a duk wata sai mun ciwo bashi muke biyan ma’aikatanmu albashi, tun da na zo a matsayin shugaban karamar hukumar, sau hudu kawai na iya biyan albashin ma’aikata ba tare da ciwo bashi ba,” inji shi. Ya ce “A lokacin da muka karbi shugabancin wannan karamar hukuma ana bin ta bashin sama da Naira miliyan 300, ya kamata a ce mun rage bashin amma abin ya gagara. Kuma mu ’yan siyasa ne don haka muna son mu ga mun dadada wa jama’a, babu yadda za a yi a ce akwai kudi amma mu ki taimaka wa jama’a.” Shugaban ya ce a yanzu kunya yake ji ya shiga jama’a saboda “Ni ne na samu goyon bayan jama’a fiye da duk shugaban da aka yi a karamar Hukumar Lere. Amma kuma ni ne na fi kowa matsala, saboda kowa yana ganin tunda na zo komai zai gyaru,” inji shi. Ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar su kara hakuri kan wannan hali da ake ciki har zuwa lokacin da Allah zai warware matsalolin.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi