karamar magana za ta zama babba

Idan akwai wanda ke shakkun cewa ba  Shugaba Goodluck Jonathan ne ke mulkin kasar nan ba to sai ya daina, domin kuwa ta bayyana karara cewa yana bin umurnin iyayen gidansa ne, wadanda suka dora shi bisa kujerar mulki don dai kawai su yi ta karkata shi zuwa ga son ransu. Wadannan iyayen gidan nasa […]

karamar magana za ta zama babba
karamar magana za ta zama babba

Idan akwai wanda ke shakkun cewa ba  Shugaba Goodluck Jonathan ne ke mulkin kasar nan ba to sai ya daina, domin kuwa ta bayyana karara cewa yana bin umurnin iyayen gidansa ne, wadanda suka dora shi bisa kujerar mulki don dai kawai su yi ta karkata shi zuwa ga son ransu. Wadannan iyayen gidan nasa kuwa makiyan wani sashen kasar nan ne, kuma ba su kaunar  ganin kowa da kumbar susa sai dai su-ya-su.  Shi ya sa a makon jiya halinsa ya fito fili sa’ilin da ya yi furuci mai tayar da hankali game da yajin akin da kungiyar malaman jami’o’i ke yi don neman inganta harkokin ilmi a jami’o’i ta yadda da za a magance tabarbarewar da ke hana  ‘ya’yanmu samun ilmi mai armashi.  Makiya zaman lafiya a Najeriya sun kitsa masa,  wai ba wannan ne dalilin da ya sa malaman jami’o’in ke yajin aikin ba, a’a, makiya gwamnatinsa ne daga wani sashen kasar nan ke neman dagula masa lissafi ta yadda za a ga wallensa, a kuma shafa masa kashin kaji don kar ya ji dadin shugabancin kasar nan.
Wannan ba abin mamaki ba ne ga wadanda suka fahimci irin tsananin kiyayya da karar tsanar da mutanen yankin gabashin kasar nan, musamman ma mutanen Shugaba Jonathan, suka dorawa mutanen Arewa, balle ma Musulmin cikinsu. Hakan kuma ya bakanta zukatansu, ba su tunanin komai sai yadda za su cuci yankin Arewa da kuma yadda za su kai jama’arta su baro a banza. Mutanen Shugaba Jonathan, wadanda ke yi wa Yahudu da Nasara kore na son yin amfani da wannan yajin aikin don kara habaka matsalolin da ke neman rarraba kawunan jama’a domin ta haka ne kawai za su ji dadin daurewa Jonathan gindi ya  ci gaba da bin tafarkin Turwa na muzgunawa wani sashen kasar nan da kuma dakile abin da suka yi imani da shi.
Dangane da haka ne ake kokarin tadiye kungiyar malaman jami’o’in ta hanyar rarraba kawunan ‘ya’yanta bisa tafarkin kabilanci da kuma addini, domin kuwa an rigaya an nunawa Shugaba Jonathan cewa ‘yan Arewa ne ke kokarin kai shi kasa ta hanyar yin amfani da wannan yajin aikin, aka kuma nuna masa cewa wajibi ne ya dauki matakin da ya dace wajen maganinsu da kuma raba  kawunansu don kada su yi tasiri.
Shi ya sa aka zuga shugabannin jami’o’in kasar nan, watau bice Chancellors, don su yi taro da niyyar yi wa  kungiyar malaman jami’o’i yankan baya  don a bubbude jami’o’in, aka kuma tsorata su da batun kora idan ba su koma bakin aiki ba bayan cikar wa’adin da aka diba masu.
Bayan sun yi wannan taron ne sai mai rike da mukamin Ministar Ilmi, Chief Nyesom Wike ya fito fili, kiri-kiri, ya bayyana ra’ayin mataimakan shugabannin jami’o’in , ya kuma nuna cewa hakan shi ne wajibi domin ba za a bari malaman jami’o’i su kai gwamnati kasa ba. Amma daga bisani sai ga shi nan Shugaba Jonathan ya ce gwamnatinsa ba ta yi barazanar korar malaman jami’o’i ba idan har ba su koma bakin aikinsu ba, domin ba a rufe kofar  tattaunawa da su game da janye yajin aikin ba. Bayanin da Shugaba Jonathan ya bayar game da haka ya ba kowa mamaki, domin kuwa  tun can farko cewa ya yi ba gwamnatinsa ce ta ce haka ba, wannan ra’ayin mataimakan  shugabannin jami’o’i ne wanda  Ministan Ilmi ya yi zarbabiya wajen bayyanawa.
A’aha! Tsakanin mataimakan shugabannin jami’o’i da Ministan Ilmi wane ne ke bayar da umurni ga wani? Ai ko ba a fada ba an san cewa Minista ne gaba da su,  domin jami’o’i a karkashin ma’aikatarsa suke. To shi ne kuma sai a ce ya zama kakakinsu maimakon na shugaban kasa?  Baicin haka nan  wane ne ya sanya mataimakan shugaban jami’o’i yin taron idan ba Ministan Ilmi ba, tun  da dai a karkashinsa suke? Kuma Ministan Ilmi na iya yin zarbabiyar furta batun korar malaman jami’o’in ba tare da sani ko iznin shugaban kasa ba? Ina! Wane mutum, in ji mutuwa?
Ana iya cewa Shugaba Jonathan ne dai ya yi kidansa, ya kuma yi rawarsa daidai da yadda mutanensa, ‘yan koren Yahudu da Nasara, suka kitsa masa da niyyar bata mutuncin wasu ‘yan Arewacin Najeriyar da  ba su kauna. Gashi nan ma dangane da haka wasu jami’o’i da manyan makarantu a Jihar Enugu da kuma ta Edo sun umurci malaman jami’o’insu su kuma bakin aiki, su ci gaba da koyar da dalibai. To ashe ke nan ana iya cewa an kama hanyar nuna wa duniya cewa malaman Kudanci na da niyyar janye yajin aiki, na Arewa ne ba su son a yi haka don su yi fito-na-fito da gwamnatin Jonathan.
To, Idan har gwamnatin Jonathan, wacce ‘yan kudu maso kudu ke garawa kamar gare-gare, ba ta dauki matakan kawar da kabilanci da nuna bambancin addini da jama’ar yankin gabashin kasar nan suka zake a kansu ba, to ba shakka hakan zai bude idanuwan sauran al’ummomin kasar, kuma karamar magana za ta zama babba, domin kuwa ai ba iya kwanciya aka fi kare ba, sai dai a gwada masa mayafi.