Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah
Abubuwan da ake bukatar Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022
A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan.
A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan:
Kabbarori:
Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi.
Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd.
Zakkar Kono:
Wajibi ne ga duk wanda ke da hali ya fitar wa kansa da sauran wadanda yake ciyarwa Zakkar Kono a lokacin Karamar Sallah, kafin a yi sallar idi.
Mutum zai fitar wa kansa da kowane wanda yake ciyarwa Sa’i daya (Mudun Nabi 4) na abin da aka fi amfani da shin a abinci a inda yake.
Malamai sun ce za a iya fitarwa tun biyu uku kafin ranar Sallah, amma wajibcinta na farawa ne daga ranar Sallah.
Ana bayarwa ne kafin sallar idi, wanda ya bayar kuma bayan sallar idi, to ta zama sadaka kamar sauran sakakoki.
Wankan idi:
Ana so mutum ya yi wankan ibada kafin zuwa sallar idi a ranar Sallah. Siffar wankan daya ce da sauran wankan ibada.
Sabbin kaya:
Ana so mai zuwa idi ya sanya sabbin tufafi ko mafiya kyawun kayans.
Sahabin Manzon Allah (SAW), Abdullahi Ibn Abbas (RA) ya ce Manzon Allah na da wata alkyabba da yake sawa a ranar idin Karamar Sallah.
Imam Al-Baihaki ya ruwaito cewa Ibn Umar kan sanya mafiya kyawun kayansa a ranar idi.
Turare:
Ana bukatar maza su fito cikin ado su sanya turare domin tafiya sallar idi.
Cin abinci:
Ana so mutum ya ci abinci kafin tafiya sallar idi a Karamar Sallah.
Hadisi ya nuna Manzon Allah (SAW) yakan ci dabino (adadin mara) kafin ya tafi idi a ranar Karamar Sallah. Wanda bai samu dabino bai zai iya cin wani abun.
Zuwa sallar idi:
An fi so mutum ya taka zuwa masallaci, a kan lokaci, yana tafiya, yana yin kabbarori.
Ana zuwa sallar tare kananan yara da mata har da masu jinin al’ada, amma dai za su kebe daga gefen sahu.
Babu kiran Sallah ko nafila:
Ba a yi wa sallar idi kiran sallah sannan ba a yin nafila – zama kawai za a yi ana kabbarori a jira isowar liman.
Abdullahi bin Abbas ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya yi sallar Idi raka’a biyu, bai yi wata sallah (ta nafila) ba kafinta ko bayanta.”
Jabir bin Abdullahi ya ruwaito Hadisi cewa, ba a kiran sallah ko ikama kafin ko bayan sallar idi.
Siffar sallar idi:
Duk da cewa Sallar Idi ba farilla ba ce, ana yin ta ne a jam’i. Raka’a biyu ce kamar kowace sallah mai raka’a biyu kuma a bayyane ake yin ta jim a lokacin Walha.
A raka’ar farko ana yin kabbarori shida bayan Kabbarar Harama. Raka’a ta biyu kuma ana yin kabbara biyar bayan kabbar mikewa zuwa raka’ar.
Sauraron huduba:
Bayan an idar da sallar idi ana bukatar masallata su jira su saurari hudubar liman, kuma laifi ne yin magana a yayin da ake huduba.
Taya murna:
Ana bukatar Musulmai su taya juna murna da fatan alheri a ranar Sallah.
Jubayr ibn Nufair ya ruwaito cewa Sahabbai kan yi wa junansu addu’ar Allah Ya karba musu ibadun da suka yi gabanin ranar.
Sauya hanya:
Koyarwar Manon Allah (SAW) mutum ya sauya hanya idan zai koma gida daga sallar idi.
Zumunci:
Sada zumunci da faranta wa juna rai da abubuwan alheri na daga cikin abubuwan da ake bukata a ranar idi.
Barka da Sallah!