Karamar Sallah: Sufeta Janar na ‘Yan sanda ya bada umarnin inganta tsaro

Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya (IG) Mohammed Adamu, ya umarci mataimakansa da Kwamishinonin ‘yan sandan jihohi a shiyyoyi da jihohin kasar da su tabbatar da inganta tsaro lokacin bukukuwan karamar Sallah da za a yi. Kakakin hedkwatar hukumar ‘yan sanda kuma Kwashinan ‘yan sanda Frank Mba, ya bayyanawa manema labaran hakan yau a Abuja. […]

Karamar Sallah: Sufeta Janar na ‘Yan sanda ya bada umarnin inganta tsaro

Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya (IG) Mohammed Adamu, ya umarci mataimakansa da Kwamishinonin ‘yan sandan jihohi a shiyyoyi da jihohin kasar da su tabbatar da inganta tsaro lokacin bukukuwan karamar Sallah da za a yi.

Kakakin hedkwatar hukumar ‘yan sanda kuma Kwashinan ‘yan sanda Frank Mba, ya bayyanawa manema labaran hakan yau a Abuja.

Frank, ya ce an umarci jami’an ‘yan sandan da su tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi, wuraren shakatawa da wajen bauta.