Karamar yarinya ta goga wa likitoci coronavirus

Ma’aikata lafiya takwas sun kamu da cutar coronavirus bayan mu’amala da suka yi da wata yarinya ‘yar shekara biyu mai dauke da cutar a jihar Ogun. An killace likitoci da ma’aikatan jinya da na gudanarwa takwas din da suka kamu da cutar a Babban Asibitin Tarayya da ke Abeokuta, jihar Ogun. Sanawar da hakan da […]

Karamar yarinya ta goga wa likitoci coronavirus

Likitan Najeriya

Ma’aikata lafiya takwas sun kamu da cutar coronavirus bayan mu’amala da suka yi da wata yarinya ‘yar shekara biyu mai dauke da cutar a jihar Ogun.

An killace likitoci da ma’aikatan jinya da na gudanarwa takwas din da suka kamu da cutar a Babban Asibitin Tarayya da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Sanawar da hakan da asibitin ya fitar da ce an gano sun kamu da cutar ne bayan gwajin da aka yi wa wadansa suka yi mu’amala da karamar yarinyar a cikin ma’aikata.

Sanarwar, dauke da sa hannun Segun Orisajo, mai magana da yawun asibitin ta ce “Duk da haka, har yanzu babu wanda ya nuna alamun cutar coronaviru daga cikinsu.

“Shugaban sibitin, Farfesa Adewale Musa-Olomu ya ce ko da yake ma’aikatan ba su nuna alamun cutar ba, dukkansu an umurce su da killace kansu kuma an fara duba lafiyarsu”, inji shi.

Ya yi musu addu’ar samun sauki cikin gaggawa da kuma jaddada kurin asibitin ta kare lafiyar ma’aikata da marasa lafiya.