Karamar yarinya ta mutu a rijiya a Kano

Wata yarinya mai shekara 10 ta mutu bayan da ta fada cikin wata rijiya a kauyen Yanka Tsari da ke Karamar Hukumar Dawakin Kudu a  Jihar Kano. Yarinyar mai suna Binta Shehu ta zame ta fada a rijiyar rijiyar ce bayan da ta je diban ruwa, kafin daga baya aka ceto ta a sume. Da […]

Karamar yarinya ta mutu a rijiya a Kano

Wata yarinya mai shekara 10 ta mutu bayan da ta fada cikin wata rijiya a kauyen Yanka Tsari da ke Karamar Hukumar Dawakin Kudu a  Jihar Kano.

Yarinyar mai suna Binta Shehu ta zame ta fada a rijiyar rijiyar ce bayan da ta je diban ruwa, kafin daga baya aka ceto ta a sume.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saidu Ibrahim, ya ce da misalin karfe 2:20 na yammacin ranar Laraba, wani mutum mai suna Musa Ibrahim ya sanar da hukumar afkuwar lamarin.

“An aike da jami’an ba da agajin gaggawa, inda suka ceto yarinyar a sume kafin daga bisani ta ce ga garinku nan.

“An mika gawarta ga Dagacin kauyen, Junaidu Alasan a madadin danginta”, inji jami’in.

Daga karshe ya shawarci jama’a da su rika yi wa rijiyoyin da suke ginawa murafa don kar a rika fadawa a ciki.