karamin minista ba mai zaman banza ba ne – Umaru Dambo
Aminiya: Ranka ya dade meye bambancin babban minista da karami? Umaru Dambo: Babu wani bambanciba na a-zo-a-gani, bambancin ya danganta ne ga amincewar da shi shugaba ya yi wa wanda ya zaba da kuma kwarewarsa da iya aikinsa, don haka bambancin ba wai na kudi ne ko na wani abu daban ba. Kamar ni a […]

Aminiya: Ranka ya dade meye bambancin babban minista da karami?
Umaru Dambo: Babu wani bambanciba na a-zo-a-gani, bambancin ya danganta ne ga amincewar da shi shugaba ya yi wa wanda ya zaba da kuma kwarewarsa da iya aikinsa, don haka bambancin ba wai na kudi ne ko na wani abu daban ba. Kamar ni a lokacin da na yi karamin minista a ma’aikatar man fetur, nine ke kula da duk albarkatun man da ake tacewa a nan kasar da kuma duk wani wurin tara mai (depot) a kasar nan, shi kuma babban minister shi ne mai kula da duk wani mai da ake fita da shi kasashen waje. Don haka kusan aikin iri daya ne, sai dai an raba ne don a samu saukin gudanar da aikin da gano duk wani hali da aikin ke ciki, amma kusan tare ake kuma tare ake komai, tun da su ma’aikata ne masu kare komai. Don haka bambancin ba wani yawa, kuma kowanne yana bayar da gudunmawa.
Kuma shi minista da kake gani, wani ginshiki ne amintacce kuma garkuwa ga gwamnatin da yake wa aiki a ma aikatar da aka tura shi, kasancewarsa minista a ma’aikatar da yake zai kare duk wata cuta da kuma duk wani abu wanda yake ba daidai ba a ma’aikatar, kuma shi ne kamar garkuwa na gwmanati a wajen, kuma duk wani tsare-tsare na cigaba da ake so a kawo a ma’aikatar domin taimaka wa al’ummar kasa to shi ne zai dauka ya gabatar wa da gwamnati, bayan su ma’aikata sun gama tsarawa.
Kuma minista yana da matukar mutuncin kwarai ga gwamnati, domin shi ne wakilin gwamnati a ma’aikatar da za a tura shi, don haka zai hana duk wata cuwa-cuwa da kuma almundahana da ake aiwatarwa a ma’aikatar da yake, kuma shi zai kawo duk wata cigaba da ake so a ma’aikatar da yake, domin cigaban kasa da al ummarta, don haka minista babban amintaccen shugaban kasa ne, kuma duk wanda ka ga an nada to an amince da shi, domin shi ne wakilin shugaban kasa a inda yake.
Aminiya: Meye amfanin nada ministan bulayi, wato wanda bai da ofis?
Umaru Dambo: To ni a ganina ministan da ba shi da ofis ai bai da wani amfani, kuma ban ga alamar akwai shi a cikin wannan tsarin ba, domin duk wanda aka dauko aka ba shi minista ya kamata a ce an ba shi abin yi, kuma abin nan wanda zai taimaka wa kasa ne, ba wai kansa ba kawai, don haka ina ganin ai ba ma wannan tsarin.
Aminiya: Da za a ce ka ba da shawara a kan wannan tsari na karamin minista da babba da kuma wanda bai da ofis, me za ka ce?
Umaru Dambo: Ai na fada da farko cewa minista babba da karami a wani tsarin ya yi, domin kamar yadda na ce, ai bambancin ba yawa, kuma na kawo misali a kaina a lokacin da na rike ministan man fetur, bambancin shi ne,wannan na kula da cikin gida, wannan na kula da kasashen waje. Amma kamar yadda na fada, shi minista mara ofis, wato ministan bulayi, ba shi da wani amfani. Kuma ka sani minista shi wakili ne kuma mataimaki ga shugaban kasa a duk ma’aikatan da aka kai shi.