Karamin yaro ya salwantar da N1.2m a wayar uwarsa

Kan ta ankara ya kashe mata N1.2 wajen sayayya ta manhajar buga wasa a intanet.

Karamin yaro ya salwantar da N1.2m a wayar uwarsa

Wata uwa da ta shiga cikin tsaka mai wuya bayan da ta ba wa danta mai shekara bakwai wayarta ya buga wasa a intanet da wayar.

Matar ba ta yi aune ba sai daga baya ta lura cewa dan nata ya kashe Naira miliyan 1.238 wajen yin sayayya ta manhajar wasan a intanet da wayar tata.

Tun da farko matar ta ba wa dan nata izinin yin sayayya na wasu ’yan kudade da ta kayyade masa a wayar tata.

Sai dai ta manta wayar na hade da asusun ajiyarta, kuma dan nata ya rika amfani da wayar mahaifiyar tasa yana buga wasan yana kuma yin sayayyan ba da saninta ba.

Cibiyar bayar da shawarwari ga kwastomomi a Jihar Lower Saxonyta kasar Jamus ce ta sanar da haka a bayan da ta fitar domin bikin zagayowar ‘Ranar Aminici a Intanet’ na bana.

Sai dai wata kwararriyar a fannin shari’a a kasar ta Jamus, Kathrin Koerber, ta ce dokar kasar ba ta amince ba yara su yi sayayyar da farashinsa ya fi kudin kashewarsu, sai da izinin iyaye —saboda haka aka dauki matakin kalubalantar kudaden da aka caji matar.

Koerber ta ce, shi ya da aka aike wa kamfanin da wasikar koke kan cajin da aka yi wa mahaifiyar yaron, kamfanin ya dawo mata da kaso mai tsoka na kudin da aka caje ta na Yuro 2,644.31.

Ta bayyana cewa iyaye na yawan ba wa ’ya’yansu wayoyinsu domin debe musu kewa, musamman a lokacin annobar coronavirus.

Saboda haka ta shawarci mutane da suka rika dubawa sosai kafin su mika wa yara wayoyinsu domin guje wa aukuwar irin haka.

A ware Ranar Aminci a Intanet, wadda za a yi ta bana a ranar Talata, domin wayar da kai a kan cin zali a intanet, samun shaida ta intane da kuma kulla mu’amala ta hanyoyin zamani.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Tags