Karancin Abinci: Sheikh Yahaya Jingir ya shawarci Gwamnatin Najeriya
Har yanzu farashin kayan abinci bai fadi ba yayin da aka cinye abincin da aka ajiye.
Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su yi gaggawar sanya hannu a noman rani a bana da zimmar magance karancin abincin da ke tunkarar kasar nan.
Malamin ya yi kiran ne lokacin da yake gabatar da wa’azi a Masallacin Juma’a na ’Yan-Taya da ke birnin Jos a jihar Filato.
- Waiwaye: Yadda Shaikh Pantami ya caccaki gwamnati bayan kara farashin man fetur
- Sheikh Ja’afar da Albani sun samu karramawa
Ya ce duk da cewa an fara girbin amfanin gona a wurare daban-daban na Arewa, amma har yanzu farashin kayan abinci bai fadi ba yayin da aka cinye abincin da aka ajiye.
Sheikh Jingir ya ce: “Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da al’umma baki daya, a yi niyyar noman rani a bana.
Ta yadda noman damina na karewa, sai a shiga na rani, domin a magance matsalar yankewar abinci a Najeriya.”
Sheikh Jingir ya ce wannan gwamnati tana turo kudade domin tallafa wa manoma amma abin takaici wadanda ba manoma ne suke karbe kudaden da take turowa.
Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakan ganin ta magance matsalar domin ganin kudaden tallafa wa manoman suna zuwa hannun manoma na gaskiya.
Shehin malamin ya yi kira ga masu hali su taimaka wa talakawan kasar nan, domin a cewarsa, talakawa suna cikin mawuyacin hali hakan ya sa lallai a taimaka musu saboda akwai wadanda suke kwana ba su ci abinci ba a kasar nan.