Karancin danyen mai ya hana Matatar Dangote fara aiki

A karo na biyu an dage lokacin fara aikin matatar wadda ake sa ran za ta taimaka wajen rage matsalar karancin mai a Najeriya da wasu kasashen Afirka.

Karancin danyen mai ya hana Matatar Dangote fara aiki

Matatar Mai ta Dangote

Karancin danyen mai ya hana katafariyar Matatar Mai ta Dangote fara aiki da aka yi alkawari a watan Oktoba.

Karo na biyu ke nan da ake dage lokacin fara tace mai da aka sanya na matatar, wadda ake sa ran fara aikinta zai wadatar da Najeriya da wasu kasashen Afirka kimanin 12 da tataccen mai da dangoginsa.

Masana sun bayyana cewa zuwa ranar Talata da watan Oktoba ya kare, Matatar Dangote ba ta samu adadin danyen man da take bukata domin fara aiki ba.

Matsalar ta kuma kawo tsaiko ga fara aikin wasu kananan matatun mai biyar da ake sa ran za su taimaka wajen saukake matsalar mai a kasar.

Punch ta ruwaito Daraktan Zartarwa na Rukunin Kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin, na cewa a watan Satumba, Matatar Dangote ta sayo danyen mai daga kasar waje, kuma na sa ran jirgin farko na man zai iso Najeriya a tsakiyar watan Nuwamba da muka shiga.

Devakumar Edwin ya bayyana cewa duk da cewa kamfanin NNPC ne kadai ke kasuwancin danyen mai a madadin Najeriya, amma kamfanin ya ba wa wasu damar shigo da danyen man, amma bai bayyana kamfanonin ba.

Amma ya bayyana cewa shigo da danyen man da suke yi daga kasar waje na wucin gadi ne.

Ya kuma nan da karshen watan Nuwamba matatar za ta fara aiki, kuma samar da ganga 370,000 wanda zai taimaka wajen rage matsalar karancin man fetur da man dizel a Najeriya.

A watan Agusta dai NNPC ta ce ta kulla yarjejeniyar Dala biliyan 3 da bankin Afrexim, bisa alkawarin da hakan kamfanin zai biya wasu basukan da bankin ke bi.

Babban Limamin Minna Sheikh Isa Fari ya rasu

Saudiyya ta ɗauki malamai dubu 9 domin koyar da kaɗe-kaɗe a makarantu

‘Yar China na fuskantar saki bayan ta haifi jariri baƙar fata

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga