karancin kayan aikin shari’a ke haddasa cunkoso a gidajen yari – Babbar Joji
Babbar Jojin Jihar Neja Mai Shari’a Fati Lami Abubakar ta ce yawan dage kararrakin da ake a kotuna da rashin isassun kayan aikin da lauyoyi da alkalai za su yi amfani da su, domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata suna daga cikin manyan matsalolin da ake fama da su a fannin shari’a, wadanda kan […]
Babbar Jojin Jihar Neja Mai Shari’a Fati Lami Abubakar ta ce yawan dage kararrakin da ake a kotuna da rashin isassun kayan aikin da lauyoyi da alkalai za su yi amfani da su, domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata suna daga cikin manyan matsalolin da ake fama da su a fannin shari’a, wadanda kan haddasa cunkoso a gidajen yarin da ke fadin kasar nan baki daya.
Ta fadi haka ne lokacin da take jawabi a wurin wani taron da kungiyar Alkalai ta kasa ta shirya a Minna, inda ta jaddada cewa wasu daga cikin matsalolin da ake fuskantar sun biyo bayan sakacin da lauyoyi suke nunawa a wannan fanni na shari’a, don kuwa ba su shirin da suka hada da karatu da bincike a kan kararrakin da ke gabansu kafin su je kotu domin yi wa alkalai bayanai masu gamsarwa.
Ta yi kira ga hukumomin da ke da hannu cikin wannan lamarin da su tabbata an samar da isassun kudi da kayan gudanar da ayyukan da ke da nasaba da ceton jama’a daga halin da suka samu kansu a ciki. Ta nuna wasu daga cikin wadanda suka samu kansu a gaban alkalai da mutane ne wadanda tsautsayi ya rutsa da su don haka suke da fatan samun ’yancinsu ta wanke su daga zargin da ake yi musu, sai dai sakacin lauyoyi kan sa irin wadannan mutanen kan samu kansu a gidan yari.
Shugaban kungiyar Alkalai Ta kasa, Alhaji Zakariya’u Adamu ya bayyana wasu daga cikin kalubalen da ’ya’yan wannan kungiyar ke ci gaba da fuskanta, wadanda suka zame musu karfen kafa yayin da suke bakin kokarinsu wurin sauke nauyin da ke kansu na tabbatar da duk wanda aka gurfanar a gabansu ya samu hukunci daidai da abin da ya aikata. Matsalolin sun hada da rashin samar wa alkalai ababen hawa don zuwa wurin aiki yadda ya kamata da rashin samar wa bangaren shari’a ’yancin gudanar da harkokinsa yadda ya kamata.