Karancin Kudi: An kashe mutum 4 an kona bakuna a Kudancin Najeriya
An kashe mace mai shayarwa da wasu mutum uku, an kona akalla bankuna hudu a rikicin karancin sabbin kudi a jihohin Oyo, Edo da Delta
An kashe mutum hudu ciki har da mace mai shayarwa, an kona akalla bankuna hudu a rikicin da ya barke kan karancin sabbin takardun Naira a Kudancin Najeriya.
Mai shayarwar ta rasu ne bayan harsashi ya same ta a wani ATM da take bin layin cirar kudi, sauran mutum ukun kuma sun rasu ne a rikicin da ya barke bayan masu neman sabbin kudi sun yi dafifi a Ofishin Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Jihar Edo.
- Mutumin da aka yi kuskuren daurewa shekara 28 ya shaki iskar ’yanci
- Buhari ya gana da Tinubu a Aso Rock
Bankuna shida da suka hada da UBA, First Bank, Keystone, Access bank, Unity da Polaris na daga cikin wadanda masu boren suka farfasa wa tagogri tare da lalata musu ATM a jihar.
Aminiya ta gano cewa biyu daga cikin mamatan an kashe su ne a kan titin Akpakpava da ofishin na CBN yake, na ukun kuma ya gamu da ajalinsa ne a titin Sakpoba.
Ita macen ta hudu kuma harsashi ne ya same ta, amma ba ita jami’an tsaro suka nufa da harbin ba.
Rikicin ya barke ne bayan masu neman sabbin kudaden sun yi zargin wata mota da suke saton daga gidan gwamnati take ta nemi shiga harabar CBN din don neman sabbin kudi.
Sai mutanen suka ki amincewa, suka fara jifan ta, wanda hakan ya haifar da hatsaniya kafin daga bisani jami’an tsaro su shawo kan lamarin.
Wani ganau ya rikicin ya kazance ne bayan wadanda da ke titin Sakpoba sun shiga cikin yamutsin, inda abin ya rikide zuwa kai fa bankuna da shaguna hari.
An kona bankuna 4 a Delta
A Jihar Delta kuma, bata-gari sun kona bankuna akallla hudu don nuna fushinsu kan karancin takardun kudi a Kanana Hukuomin Udu, Effurun kuma Warri da ke Jihar Delta.
Aminiya ta gano cewa bata-garin sun banka wa gine-ginen bankunan Union da kuma Access/Diamond wuta, tare da kona motoci hudu tare da lalata allunan tallar ’yan siyasa a tarzomar.
“Yanzu haka bankin Access da ATM na First Bank na ci da wuta, an kone su, an nufi Ecobank da sauran bankunan, su ma su ji a jikinsu kan abin da suke yi mana,” in ji wani mazaunin yankin, Martins Alala.
Matasan sun tare hanya tare da kona wasu motoci hudu , suka kuma lalata allunan yakin neman zabe ’yan siyasa, tare da barazanar kaurace wa zaben da ke tafe.
Martins Alala, ya ce: “Mu ’yan kasa ne masu zanga-zangar adawa da karancin sabbin takardun Naira da kuma kin amincewa da karbar tsofaffin takardun naira.
“Muna fada da babbar murya cewa idan har babu kudi ba za mu yi zabe ba, mun lalata duk allunan zabe da ke nan, ba ma son ganin wani dan siyasa, duk daya suke.”
Jama’a sun shiga zullumi da ganin bata-garin sun fantsama a kan tituna domin nuna fushinsu kan halin kuncin da mutane da dama ke fuskanta a sakamakon rashin sabbin kudaden.
Amma wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, “Sojoji na harbe-harbe babu kakkautawa, sannan an girke ’yan sanda domin tsaron bankuna a yankunan Udu, Effurun da kuma Warri.”
Wata majiya ta ce tun kafin tarzomar “Bankuna, ofisoshi da masu shaguna suka rurrufe a yankunan kuma babu kudi a ATM.
“Kazalika ’yan kasauwa da gidajen mai da masu ababen hawa sun daina karbar tsoffin takardun kudi.
“Kwastomomin banki sun fara zanga-zangar ce saboda bankuna sun ki ba su sabbin takardun kudi.
“Lamarin ya haifar da fargaba a yankunan kananan hukumomin Warri, Udu da Effurun, inda bankuna suka rurrufa.
Zanga-zanga ta tsayar da komai a Ibadan
A Jihar Oyo kuma, daruruwan fusatattun masu zanga-zanga a birnin Ibadan sun toshe wasu manyan hanyoyi da ya haifar da cunkoson ababen hawa.
Masu zanga-zangar sun nuna matukar bakin ciki da damuwa ne a game da matsalar karancin kudi a hannun jama’a da kuma wahalar fetur da tsadar shi.
Aminiya ta gane wa idanunta yadda al’amuran yau da kullum suka tsaya cik a birnin na Ibadan da kewaye a inda wasu ’yan kasuwa suka fara rufe kantuna.
Wasu makarantun firamare da sakandare sun bayar da umarnin rufewa tun kafin lokacin da aka saba rufe su.
Aminiaya ta gano cewa an fara zanga-zangar ce da misalin karfe 8 na safe a kan babbar hanyar Ologuneru a Unguwar Eleyele kusa da Hedkwatar ‘yan sanda a Jihar Oyo da ta bazu zuwa Unguwar Mokola da hanyar Sango zuwa Kwalejin Kimiya da Kere-kere da kuma Kasuwar Bodija.
An girke jami’an tsaro a wurare domin tabbatar da zama lafiya da kwanciyar hankali.
Wannan ita ce zanga-zanga ta uku da aka yi a Ibadan a kan wannan matsala ta karancin kudi a hannun jama’a da kuma karancin man fetur da tsadar shi.
An yi zanga-zangar farko ne a ranakun Juma’a da Asabar da Litinin a makon farko na watan Fabrairu da muke ciki.
Zanga zangar ta farko ce ta haifar da dakatar da yin gangamin yakin neman dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Ibadan a ranar 7 ga wannan wata na Fabrairu.
Jam’iyyar APC a Jihar Oyo ta tsayar da Alhamis 16 ga watan Fabrairu a matsayin sabuwar ranar taron a Ibadan.