Karancin kudi: An kona bankuna 10 rana guda a Ogun
Akalla bankuna 10 aka kona a tarzomar da ta barke a Jihar Ogun kan karancin takardun kudi.
Akalla bankuna 10 aka kona a tarzomar da ta barke a Jihar Ogun kan karancin takardun kudi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce hakan kari ne kan kona tashar kamfanin rarraba wutar lantarki ta IEBDC da kuma saktariyar majalisar dokokin jihar da matasan suka yi.
- Zaben 2023: Za ta dauki mataki kan masu murkushe dimokuradiyya a Najeriya —Birtaniya
- JAMB ta dakatar da rajisar daliban DE har sai baba ta gani
Aminiya ta rawaito cewa zanga-zangar ta fara ne daga kofar fadar Akarigo na Romeland, da Oba Babatunde, inda matasan suka rufe hanyoyi suka kuma hau cinna wutar.
Ta shafinsa na Twitter Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Muyiwa Adejobi ya ce matasan da suka yi wannan aika-aika, ba su yi aiki da hankali ba, kuma babu wayewa a lamarinsu.
“Kusan bankuna 10 sun kone kurmus, haka tashar wutar lanatrki ta IEDC, ina dalili? Mun fara kamo su, kuma za mu ci gaba, duk inda suke za mu kamo su, mu gurfanar da su gaban kotu.” in ji shi.
Shi ma gwamnan jihar, Dapo Abiodun, a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido ya yi alkawarin tallafi ga wadanda suka yi asara da kuma tabbatar da an hukunta waɗanda suka yi barnar.