karancin kudi shi ne kalubalen da ke fuskantar ilimin – Farfesa Muhammad
Wani kwararre a fannin ilimi, Farfesa Umar Tuni Muhammad ya ce rashin ware kaso mai tsoka tare da kashe kudi a harkar ilimi su ne suke sanyawa bangaren ilimi yake fuskantar kalubale a kasar nan. Farfesan ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a cikin makon da muke ciki.Ya ce, […]
Wani kwararre a fannin ilimi, Farfesa Umar Tuni Muhammad ya ce rashin ware kaso mai tsoka tare da kashe kudi a harkar ilimi su ne suke sanyawa bangaren ilimi yake fuskantar kalubale a kasar nan.
Farfesan ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a cikin makon da muke ciki.
Ya ce, da a ce gwamnati za ta rika kashe kaso mai tsoka a harkar ilimi, da babu shakka za a cin ma burin da ake so a bangaren ilimi a kasar nan.
“Amma matsalar ita ce ba a ware kaso mai tsoka ga bangaren ilimi kuma ba a kashe kudin da suka kamata. Wannan shi ke sanyawa muke fuskantar kalubale da matsaloli a bangaren ilimi a kasar nan.” Inji shi.
A ganinsa, da gwamnati za ta rika sanya ido ta tabbatar da cewa duk kudin da aka ware an kashe su kamar yadda ya kamata a harkar ilimi to abubuwa za su inganta.
Ya bayyana cewa matsalar da ake fuskanta a bangeren ilimi ta fi yawa a Arewacin Nijeriya.
Saboda haka sai ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen tunkarar kalubalen da ke addabar ilimi a kasar nan.
Ya dage a kan cewa sai gwamnati ta dukufa wajen ganin jihohi sun ci gaba da bin turbar da aka dauko ta maganin kalubalen yaran da ba su zuwa makaranta.
A ganinsa ilimin almajirai na zamani da aka bullo da shi da ciyar da yara dalibai a makarantu hanya ce da za a inganta harkar ilimi a kasar nan.
Sai dai kuma ya yi kira ga gwamnati ta kara malamai a makarantu tare da inganta albashinsu don su ji dadin koyarwa.
Ya ce, shi ya sa suka bai wa gwamnati shawara ta fuskanci matsalolin da suke damun ilimi da gaskiya da rikon amana tare da samar da kayayyakin aiki.