karancin mai: DPR ta rufe gidajen mai 39 a Kano
Sashen kula da albarkatun man fetur watau DPR ya rufe gidajen mai 39 cikin makonni biyu a Jihar Kano saboda samun su da laifin sayar da mai sama da farashin da doka ta tanada.Jami’in sashen mai kula da shiyyar Kano, Alhaji Isa Tafida ne ya sanar da haka ga manema labarai ranar Talatar da ta […]
Sashen kula da albarkatun man fetur watau DPR ya rufe gidajen mai 39 cikin makonni biyu a Jihar Kano saboda samun su da laifin sayar da mai sama da farashin da doka ta tanada.
Jami’in sashen mai kula da shiyyar Kano, Alhaji Isa Tafida ne ya sanar da haka ga manema labarai ranar Talatar da ta gabata, a karshen zagayen da ya yi don duba yadda ake sayar da mai a fadin jihar.
Alhaji Isa Tafida ya bayyana cewa za a ci gaba da rufe gidajen mai muddin dai suna karya dokar sayar da shi ko boye shi da nufin cin kazamar riba.
Matsalar albarkatun man fetur ta dade tana addabar al’umar kasar nan, kuma masu ruwa da tsaki suna bakin kokarin su wajen ganin al’amurra sun gyaru amma wasu tsiraru suna yin zagon kasa ga kokarin da ake yi na kawar da wannan matsala ta man fetur.
Sai dai mafiya yawan al’umomin da Aminiya ta zanta da su watau direbobi da masu yin tafiye-tafiye sun bayyana cewa ya kamata a rika yin horo mai tsanani kan duk wanda aka samu da laifin boye man.