karancin mai: Fasinjoji da direbobi sun koka a Jihar Legas
A ’yan kwanakin nan ne man fetur ya yi karanci a jihar Legas, inda masu ababen hawa suka ci gaba yin dogon layi a gidajen mai, hakan ya sa fasinjoji da direbobin bas da masu motocin kansu suka yi kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace don yin maganin matsalar a jihar da […]
A ’yan kwanakin nan ne man fetur ya yi karanci a jihar Legas, inda masu ababen hawa suka ci gaba yin dogon layi a gidajen mai, hakan ya sa fasinjoji da direbobin bas da masu motocin kansu suka yi kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace don yin maganin matsalar a jihar da ma Najeriya.
Binciken Aminiya ya gano cewa yawancin gidajen mai da ke yankin Ikeja da Agege da Egbeda da Alaba da Alimosho da Aja da kuma Ekpe sun rufe, inda wadansu kalilin da ke yankin Apapa da Oshodi da Ojuelegba da Maryland da Mil 12 da suke sayar da man sun cika makil da motoci da jama’ar da suke son sayen man.
Wasu da dama daga cikin gidajen man suna sayar da man daga Naira 110 zuwa Naira 120 a kowace lita daya a ranar Litinin a maimakon Naira 87 kowace lita a farashin hukuma.
’Yan bunburutu sai cin karensu suke yi babu babbaka inda suke sayar da man yadda suka ga dama ba tare da wata fargaba ba.
Wani direba mai suna Lateef Oyewole ya ce: “Babu shakka mun shiga wani hali saboda karancin mai. Harkokinmu sun tsaya cak. Muna sayen mai da tsada, muna daukar fasinjoji da tsada. Wannan abu abin takaici ne. A ce a kasarka kana sayen arzikin da kasarka take fitarwa da tsada. Ba ma tsadar ba sai ka sha wahala kafin ka samu arziki. Wannan abun Alla-wadai ne. Muna kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace don kawar da matsalar.”
Wata fasinjar bas da ta shiga mota daga Agege zuwa layin First- Gate da ke yankin Ikeja, Misis Folarinsho Egbalaje ta ce “Babu shakka karancin mai ya sa da kyar mutum yake samun motar da zai shiga. Kuma ma idan ka samu ka shiga da kokawa, za ka biya kudin motar da tsada. Daga Agege zuwa Firsta-Gate Naira 50 kafin wannan lokaci, amma yanzu sai ka biya Naira 100 ko Naira 150.”
Sai dai shugaban kungiyar manyan ’yan kasuwa da ke sayar da man (MOMAN), Mista Obafemi Lawore ya ce dalilin da ya sa suka rage kawo man shi ne mafi yawan ’yan kasuwar bashin bankuna ya yi musu yawa.
Ya ce da dama sun karbi bashin banki sun shigo da mai suna sayar wa gwamnati amma har yanzu ba a biya su kudinsu ba.
Sai dai kamfanin mai na NNPC ya ce ya samar da lita miliyan 688 a kasuwannin kasar nan don magance matsalar da ake ciki.