Karancin mai na bazuwa a jihohi

Wani bincike da  Aminiya ta gudanar ya gano karancin man fetur yana bazuwa jihohin kasar inda hakan ya janyo dogayen layi a gidajen mai yayin da farashin man ya tashi zuwa tsakanin Naira 160 zuwa Naira 180 a kowace lita. Dogayen layuka sun dawo a gidajen da ke jihohi daban-daban har da babban birnin tarayya […]

Karancin mai na bazuwa a jihohi

Wani bincike da  Aminiya ta gudanar ya gano karancin man fetur yana bazuwa jihohin kasar inda hakan ya janyo dogayen layi a gidajen mai yayin da farashin man ya tashi zuwa tsakanin Naira 160 zuwa Naira 180 a kowace lita.
Dogayen layuka sun dawo a gidajen da ke jihohi daban-daban har da babban birnin tarayya na Abuja da Kano da Legas da Sakkwato da Katsina da Borno da Anambara da Delta da kuma Kaduna inda ake sayar da man fiye da Naira 145 a kowace lita da gwamnati ta kayyade.