karancin mai ya janyo an ba hammata iska a gidajen man Legas

An ba hammata iska yayin da jama’a ke kokarin sayen man fetur a gidajen mai da dama na Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.Binciken Aminiya ya gano cewa lamarin ya auku ne gidan mai na Conoil da ke kan titin Kafitol da ke Agege da gidan mai na Total da ke unguwar Egbeda […]

karancin mai ya janyo an ba hammata iska a gidajen man Legas

An ba hammata iska yayin da jama’a ke kokarin sayen man fetur a gidajen mai da dama na Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
Binciken Aminiya ya gano cewa lamarin ya auku ne gidan mai na Conoil da ke kan titin Kafitol da ke Agege da gidan mai na Total da ke unguwar Egbeda da Forte Oil da ke titin Cement da Profel Oil da ke unguwar Pako da kuma Rain Oil da ke titin Pen Cinema.
Wani, wanda lamarin ya auku a kan idonsa a gidan man Conoil da ke kan titin Kafitol da ke Agege mai suna Musa Isyaka ya bayyana cewa lamarin ya auku ne yayin da wadansu masu motocin haya suka ki bin layi. “Muna cikin bin layi sai kawai masu motocin haya da ake kira ’yan damfo suka rika shiga ta daya kofar. Daga nan sai mutane suka fara yi wa ma’aikatan gidan man magana don su rufe kofar, amma sai ’yan damfon suka fi karfinsu suka cigaba da shiga. Sai kawai sauran mutanen da suke baya suka fusata su ma suka rika fita daga layi suna wucewa gaba, sai layi ya rikice. Kan ka ce kwabo, sai wani mai mota, cikin fushi, ya kama wani dan danfo da kokawa. Da karen motarsa ya ga haka, sai ya shiga fadan. Nan suka yi ta ba hammata iska daga baya aka raba su”. Inji shi.
Shi ma Malam Buba Garba, wanda ya ga yadda aka yi fadan a gidan man Forte Oil da ke kan titin Cement ya ce, “Muna cikin bin layin sai kawai wani mutum ya shigo cikin gidan man ya zo ya ce idan ba a ba shi mai ba zai kona kansa da gidan man. Daga nan sai wasu da suke cikin layi suka fusata suka fara zaginsa, wani kawai sai ya kai masa duka, sai kokawa ta kaure a tsakaninsu da kyar aka raba su. Daga nan sai manajan gidan man ya ba da umarnin a rufe gidan man ba tare da wani bata lokaci ba”.
Aminiya ta ga gidajen mai da dama  da ke yankin Oshodi da Ikeja da Ogba da Alimosho a rufe, wasu gidajen man kuma akwai dogayen layukan motoci suna jiran tsammani.
Shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da albarkatun iskar gas na yakin Kudu maso Yamma, Mista Tokunbo Korodo ya shaida wa manema labarai cewa, mafi yawan runbunan ajiyar mai babu komai a cikinsu. Ya kara da cewa sauran man da yake cikin runbunan ajiyar ba zai wadatar da bukatun jama’a ba.