karancin mai ya janyo tashin farashin sufuri a Legas
Ga alamu karancin mai da ake ci gaba da fama da shi a sassa da dama na Jihar Legas ya janyo tashin farashin kudin mota da baburan hawa da kashi 50 a wasu sassan har kashi 100 cikin dari. Binciken Aminiya gano cewa wuraren da masu motocin haya da masu babura suke dauka a Naira […]
Ga alamu karancin mai da ake ci gaba da fama da shi a sassa da dama na Jihar Legas ya janyo tashin farashin kudin mota da baburan hawa da kashi 50 a wasu sassan har kashi 100 cikin dari.
Binciken Aminiya gano cewa wuraren da masu motocin haya da masu babura suke dauka a Naira 50 ya koma Naira 100 sannan wuraren da ake dauka Naira 150 ya koma 200.
Aminiya ta gano cewa daga Unguwar Agege zuwa Unguwar Oshodi da kafin lokacin karancin mai ake biyan Naira 100 zuwa 150 yanzu ya zama Naira 200 wani lokaci ma har Naira 300 masu mota suke karba daga wurin fasinja.
Wani fasinja mai suna Malam Saminu Musa ya bayyana cewa masu motoci da baburan haya suna yin amfani da karancin mai suna tatsar fasinja yadda suka ga dama. “Yanzu wurin da muke biyan Naira 50 ya koma Naira 100. Wuraren da muke biyan Naira 100 ya koma Naira 200 wani lokaci ma har Naira 300 suke karba daga hannunmu. Ka san Legas babu tsayayyen farashin sufuri. Wani lokaci ma idan suka lura fasinja sun yi yawa sai su kara kamar 150 na kudin motar kuma babu wanda zai tuhume su. Da ka yi magana sai su ce idan ba za ka biya ba ka sauka ,su ma da kyar suka samu mai.” Inji shi.
Ita ma Bolanle Jami’u cewa ta yi masu haya da motoci da babura suna yi wa fasinjoji wulakanci. “Idan ka ga yadda masu mota da baburan haya suke yi mana wulakanci da yadda suke tursasa mu, gaskiya za ka tausaya mana. Ga tsadar kudin mota kuma da kun shiga sai su sauke ku duk inda suka ga dama ba tare da sun karasa da ku wurin da za ku je ba. Idan kuka yi magana sai su ce mai ya yi tsada saboda haka za su juya su je su debo wasu fasinjojin. Dole haka za ka sauka ba shiri don in ba haka ba sai su juya da ku.” Inji ta.
Amma wani direba mai suna Babatunde Rasaki ya karyata zarge-zargen da fasinjoji suka yi na yi musu wulakanci. Ya ce: “Ba ma yi wa kowa wulakanci. Ta yaya za ka wulankanta abokin huldarka. Ni dai abin da na sani shi ne karancin mai ne ya janyo karin kudin motar da muka yi saboda mu ma da tsada muke saya. Koda ka samu mai a gidan man da tsada za ka saya ballantana a wurin ’yan bunburutu’.
Shi ma wani mai tuka babur din da ake kira Marwa a Legas, Jami’u Ishola ya bayyana cewa karancin mai ne ya janyo turka-turkar da ake samu a tsakaninsu da fasinja.
Sai dai har yanzu gidajen mai dama suna sayar da man a kan farashin mai tsada wasu suna sayar da lita daya kan 110 zuwa 120 a maimakon farashin gwanati na Naira 87 a kowace lita.
Gidajen mai da dama sun kasance a rufe saboda rashin mai wasu kuwa da ke sayar da man sun ci gaba da samun layuka kodayake a wasu wurare an samu saukin dogon layin amma ana sayar da man da tsada.