karancin man fetur ya ta’azzara a Jihar Yobe
Harkokin yau da kullum na tafiyar hawainiya a sassa da dama na Jihar Yobe sakamakon tsauwalar farashin albarkatun man fetur da karancinsa da ke shirin zama alakakai ga harkokin sufuri.Aminiya ta kalato cewa tsadar man fetur da karancinsa sun fara addabar al’ummar jihar ne sama da makonni uku, domin kuwa akasarin masu gidajen man da […]
Harkokin yau da kullum na tafiyar hawainiya a sassa da dama na Jihar Yobe sakamakon tsauwalar farashin albarkatun man fetur da karancinsa da ke shirin zama alakakai ga harkokin sufuri.
Aminiya ta kalato cewa tsadar man fetur da karancinsa sun fara addabar al’ummar jihar ne sama da makonni uku, domin kuwa akasarin masu gidajen man da ke sassan jihar, musamman kamar garuruwan Damaturu da Potiskum da Gashuwa, Nguru da Gaidam duk sun rurrufe illa kalilan daga cikinsu da suka bude suke sayar da man sama da farashin da kamfanin NNPC ya amince da shi na Naira 87 kan lita guda, don aksari ma suna sayar da lita guda a kan mabambancin farashi daga Naira 100 zuwa Naira 120 a kan lita daya ta man fetur din.
Malam Umaru Potiskum wani direban karamar mota, ya bayyana wa Aminiya cewa su direbobin da ke tafiye-tafiye, abin na matukar daure musu kai, domin matsalar ita ce ba su san ma daga ina wannan matsala ta karancin mai take ba illa dai kawai a halin yanzu suna aikin ne ga masu mai kawai domin kamar shi da ya ke daukar fasinja zuwa garin Damagum, in ya zuba mai to abin da yake ragewa a cikin kudin lodin bai kai ya sayi abincin garau-garau ba.
Don haka ne malamin ya roki Gwamnatin Tarayya da kamfanin mai na kasa da su yi Allah su gano yadda matsalar take don magance ta ko jama’a sa samu sa’ida.
Shi kuwa tsohon shugaban kungiyar direbobi ta kasa (NURTW) reshen Jihar Yobe, Alhaji Hussaini Ibrahim cewa ya yi shi ya na ganin wannan matsala ta karancin mai da tsadarsa akwai lauje cikin nadi, watakila akwai masu yi wa wannan gwamnatin zagon kasa.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin daya daga dilolin mai da ke jihar, lamarin ya ci tura illa wani daga cikin kananan dilolin man, wanda shi ma ya nemi a sakaye sunansa ya ce, yadda matsalar take a ganinsa ba ta wuce karancin man da ake fama da shi ba a kasa, ba Jihar Yobe ba kadai.