karancin mata: Za a samu gwagware miliyan 30 a kasar Sin
Fiye da mutum miliyan 30 za su zama gwagware a kasar Sin saboda karancin matan da za su aura, kamar yadda kididdiga da nazarin masu bincike kan jinsin namiji da mace ke kara samun wagegen gibi.Bisa kididdigar Cibiyar kididdigar ta kasa, ta tabbatar da cewa, yawan maza ya fi na mata a kasar Sin, inda […]
Fiye da mutum miliyan 30 za su zama gwagware a kasar Sin saboda karancin matan da za su aura, kamar yadda kididdiga da nazarin masu bincike kan jinsin namiji da mace ke kara samun wagegen gibi.
Bisa kididdigar Cibiyar kididdigar ta kasa, ta tabbatar da cewa, yawan maza ya fi na mata a kasar Sin, inda a cikin mutum biliyan guda da miliyan 370, akwai mata 100 ga kowane rukuni na maza 105.02 a shekarar 2015, sannan adadin haihuwa ya nuna cewa, a kowane rukunin jarirai maza 113.51 akwai matan su 100 kacal.
Fifikon yawan jinsin maza da ake haihuwa ya fin a mata, wanda ya kama daga 103 zuwa 107 a rukunin maza, in an kwatanta da rukunin matan da ake haihuwa da yawan su yake a matsayin 100.
Sai dai abin farin ciki, a wannan al’amari, shi ne, ana samun ci gaba na raguwar gibi kusan kowace shekara, tsawon shekaru bakwai da suka gabata.
Gibin da ke tsakanin jinsi na yawan adadi, ya faro ne tun daga shekaruin 1980 zuwa 2004, inda al’amarin bambancin ya yi ta hauhawa zuwa 121.18. Wadannan alkaluma an samu karuwar su zuwa 115.8 a shekarar 2014, kafin su fara yiwo kasa zuwa adadin kididdigar da ake da shi na 113.51.
Har yanzu dai kasar Sin ke da wagegen gibi a fadin duniya a tsakanin jinsin maza da mata, kamar yadda yake kunshe a alkaluman kididdigar Hukumar Kula da lafiyar tsarin rayuwar iyali a shafin tan a intanet da ta baza a shekarar 2015.
Mafi yawan masu nazarin yadda wadannan al’amura ke wakana, sun dora alhakin faruwar lamarin, akan barin tsarin haihuwar da daya, tare da al’adar son magaji namiji; wadanda aka saba dora musu alhakin kula da iyaye idan sun tsufa, tare da hada-hadar tafiyar harkokin kasa.
Tsarin haihuwar da/’ya guda da aka shafe shekaru ana gudanar da shi a kasar, ya haifar da raguwar haihuwa, sannan nuna fifikon bukatar haihuwar da namiji ya taka rawa wajen wannan matsalar.
Alal misali, wani binciken kwananan da Jami’ar Zhejiang ta kasar Sin da Kwalejin Jami’ar Landan, sun bayyana fifita son haihuwar da namiji a kan mace, a cikin mutum 212 da aka yi nazari a kan su, wadanda shekarun su suka kama daga 18 zuwa 39.
Cai Yong, wata masaniya a harkar kididdiga, da ke Jami’ar Carolina da Chapel Hilla da ke kasar Amurka, ta yi nuni da cewa, zaman birni da neman ilimi mai zurfi, sun sanya an yi watsi da dadaddun al’adu.
Mafi yawan mazaunan birane, sukan yi ritaya daga aiki, su kuma samu fansho mai gwabi. Sannan ’ya’yan su maza ne ko mata, su aka dora wa alhakin kula da iyayen su masu nisan shekaru da suka tsufa.
Su kuwa al’ummomin da ke zaune a karkara, suna da karancin ilimi, kuma tattalin arzikin su ko samun kudin shiga ya dogara ne ga harkokin noma, duk da haka sun dogara ne ga ’ya’yan su maza, al’amarin da ke nuni da labara na daban. Wata mata da ke zaune a Lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, ta yi yunkurin halaka kanta, bayan ta sha faman fada da surukarta, inda ta rika nuna mata tsana don ta haifi ’ya’ya biyu mata.
Wani masani Farfesa die Zuoshi na Jami’ar Zhejiang, ya bayyana cewa, kima da mutumtakr darajar mace na karuwa. Kuma ya ta’allaka dalilinsa da karancin matan da za a aura a kasar, inda ya yi nuni da cewa, nan da shekara ta 2020 yawan gwagwaren maza zai kai kimanin mutum miliyan 40. A kar ta Sin an taba samun matar wani Farfesa madsanin tsimi da tanadi da ta bayar da shawarar mata su rika auren maza da yawa, inda aka yi mata caa, har aka rushe wannan batu nata.