karancin nama ya kunno kai a Kalaba
Matsalar karancin man fetur ya jefa mahauta da kuma mazauna Kalaba babban birnin Jihar Kurosriba cikin karancin nama sakamakon takaita wadata mahautan birnin da shanu da kuma kananan dabbobin da za su yanka. Bincike da Aminiya ta gudanar a tsakanin masu fataucin shanu da na awaki da kuma mahauta ta gano cewa takurawar da jami’an […]
Matsalar karancin man fetur ya jefa mahauta da kuma mazauna Kalaba babban birnin Jihar Kurosriba cikin karancin nama sakamakon takaita wadata mahautan birnin da shanu da kuma kananan dabbobin da za su yanka.
Bincike da Aminiya ta gudanar a tsakanin masu fataucin shanu da na awaki da kuma mahauta ta gano cewa takurawar da jami’an karbar kudin shiga na jangali da kuma jami’an da ke yin sintiri kan hanyoyi daga Arewa zuwa Kudu, duk da an janye shingayen tsaron nasu amma har yanzu ba ta sake zane ba. Hakan ne ya haifar da karancin dabbobin da ake yankawa.
Alhaji Yusuf Ibrahim Chaba Rawaiya, wani mahauci a Layin Sulota, mahautar Kalaba ya bayyana wa wannan jarida cewa: “Tsadar shanu da ta awaki ba babu su ba ne amma sai dai daga yanayin tsadar man fetur ne, shi ya janyo har ’yan kasuwa da mahauta suka yi tawaye, suka ce su ba za su kara sayen nama ba saboda ya yi tsada. Da aka a rage wa nama kudi daga nan sai rikici ya shiga, su kuma Fulani daga ranar su ma suka shiga taro; suka ce su ma sun janye kawo shanu kasuwa domin a saya a yanka.”
Ya ci gaba da cewa: “Tun daga wannan lokaci ba a kuma yin yankan ba, ina kyautata zato wannan mako za a kai karshen lamarin.”
Haka nan kuma wata majiya kusa da mahautan ta tabbatar cewa makwabciyar Jihar Akwa Ibom mahautan ke tafiya suke sawo shanun duk da matsananciyar tsadarsu da kuma jigilarsa zuwa Kalaba suna yankawa. dan kasuwar ya koka game da rasin ciniki da kuma tsadar kayan kasuwar tasu.
Duk da samun nasarar shawo kan matsalar karancin man fetur da aka yi, wata majiya ta shaida min cewa cikin wannan makon ake sa rai jigilar dabbobi daga Arewa zuwa Kudanci za ta kankama.
Sai dai ya zuwa rubuta wannan labara, ana ci gaba da fuskantar karancin nama a Kalaba.