karancin ruwan sha ya addabi Arewacin Kamaru
Ana fama da karancin ruwan sha a Arewacin Kamaru, musamman a rijiyoyin da jama’a ke hakawa, sabanin wadanda gwamanti da kungiyoyi masu zaman kansu ke samar wa jama’a.Mazauna yankunan karkara su suka fi shan wahala samun ruwa, don haka suke yin tafiya mai nisa kan jakuna don neman ruwa. Wadannan jakuna kuma, basu da su […]
Ana fama da karancin ruwan sha a Arewacin Kamaru, musamman a rijiyoyin da jama’a ke hakawa, sabanin wadanda gwamanti da kungiyoyi masu zaman kansu ke samar wa jama’a.
Mazauna yankunan karkara su suka fi shan wahala samun ruwa, don haka suke yin tafiya mai nisa kan jakuna don neman ruwa. Wadannan jakuna kuma, basu da su yin hanzari wurin biyar wasu bukatu na gaggawa. A wani kauye da ake kira Koudja da yake tsakanin garin Lagdo da kuma Ngong, gidajen wasu mutane ne suka kama da wuta sakamakon tartatsin wutar da ta fada a wani sashen na gidajen da ke da basassun ciyayi, aka yi musu rufi bayan an gina da tabo.
A lokacin da wannan gobarar ta fara, jama’a makota ne suka kawo dauki na dan ruwan da suke da shi, domin kashe wutar. Wata dabarar da jama’a suka yi shi ne na saukar da rufin dakunan domin saukake aikin masu kawo dauki.
A wannan lokacin da yanayin rani ya fara a duk fadin Kamaru da Arewacinta, inda yanayin rani yake daukar tsawon watanni tara (9), jama’a na shiga cikin tsanann, inda ko noman rani ma suna da matsalar samun damar yi a wasu lokuta, a dalilin zamewa tsandauri da kkasa take yi.