Karancin takardar rubutu ya jawo soke jarabawa a Sri Lanka
Lamarin ya faru ne sakamakon karancin Dalar Amurka
Hukumomin Sri Lanka sun soke jarabawar da miliyoyin daliban kasar za su rubuta sakamakon wani karancin takardar rubutu da ya kunno kai a kasar.
Lamarin ya faru ne saboda karancin Dalar Amurkan da za a yi amfani da ita wajen shigo da takardun daga kasashen waje, kamar yadda hukumomin suka tabbatar ranar Asabar.
- JIBWIS ta ziyarci Mataimakin Shugaban Kasar Ghana
- An kashe mutum 6 a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa
Hukumar Ilimin kasar dai ta ce an dage jarabawar da aka tsara yi daga ranar Litinin saboda matsalar har sai abin da hali ya yi, karo na farko ke nan tun bayan samun ’yancin kan kasar a 1948.
Sashen Ilimi na Lardin Yammacin kasar ya ce, “Shugabannin makarantu ba za su samu damar shirya jarabawa ba saboda ba su samu kudaden wajen da za a yi amfani da su wajen shigo da takardu da tawadar rubutun ba.”
Wasu majiyoyi sun ce akwai yiwuwar matakin ya shafi kusan kaso biyu bisa ukun dalibai miliyan 4.5 da za su yi jarabawar a kasar.
Jarabawar da aka dage dai na cikin gwajin da ake yi wa dalibai don tabbatar da cancantarsu ta zuwa matakin aji na gaba a makarantun kasar.
Halin matsin tattalin arzikin da kasar ta shiga dai ya kawo karancin kudaden waje da ake amfani da su wajen shigo da kayayyaki daga ketare, lamarin da ya sa yanzu haka take fama da karancin kayan abinci da man fetur da kuma magunguna.
Sri Lanka, wacce ke da kusan mutum miliyan 22 ko a farkon makon nan sai da ta sanar da cewa za ta nemi rance daga Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) don magance mawuyacin halin da take ciki.
Kazalika, kasar ta nemi wani bashin daga China, wacce daya ce daga cikin kasashen da ke ba ta bashi, ko da yake har yanzu kasar ba ta ce uffan ba a kan bukatar Sri Lankan. (AFP)