Karatun almajiranci ya haramta a Kano – Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta haramta tsarin karatun almajiranci wanda ake alakantawa da bara a fadin jihar. Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta karatun almajiranci yana mai cewa za a dauki dukkan almajiran jihar da aka dawo da su a makarantun boko. Ya ce gwamnatinsa  ta shirya daukar almajiran a makarantun firamare domin ba su ilimi na […]

Karatun almajiranci ya haramta a Kano – Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta haramta tsarin karatun almajiranci wanda ake alakantawa da bara a fadin jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta karatun almajiranci yana mai cewa za a dauki dukkan almajiran jihar da aka dawo da su a makarantun boko.

Ya ce gwamnatinsa  ta shirya daukar almajiran a makarantun firamare domin ba su ilimi na wajibi kuma kyauta a matakin farko.

Ganduje ya ce a dokar jihar Kano “Jazaman ne kowane har da almajirai a jihar Kano ya rika halartar makaranta.”

An mika almajirai ga iyayensu.

Kwamishinan Kanan Hukumomi Murtala Sule Garo ya ce jihar ta mayar da yara 1,172 da ke bara a jihar Kano zuwa jihohinsu na asali. Ita kuma an dawo mata da fiye da almajiranta 1,000.

Shugaban na Kwamitin Kwashe Almajirai a jihar ya kara da cewa sun mayar da 723 da ke bara a cikin jihar zuwa hannun iyayensu.

Almajirai 28 sun kamu da coronavirus.

A jawabinsa kan halin cutar COVID-19 a jihar, Ganduje ya ce 28 daga cikin almajiran da aka dawo da su jihar na dauke da cutar.

Ya ce tuni aka killace almajiran kuma suna samun kulawar da ta dace.