Karatun Makarantun Allo da na Boko a Arewa, ina mafita?

A farko farkon watan Yuni ne Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai kula da Ilmi da Kimiya da Raya Al`adun Gargajiya, wato UNESCO, ta fitar da wani rahotonta da ya fitar da alkalumma dalla-dalla, akan matsayin kasashen duniya bisa yawan kananan yaransu da ba su zuwa makarantun Firamare, ko kuma idan suka fara karatun Firamare din […]

Karatun Makarantun Allo da na Boko a Arewa, ina mafita?
Karatun Makarantun Allo da na Boko a Arewa, ina mafita?

A farko farkon watan Yuni ne Hukumar Majalisar dinkin Duniya mai kula da Ilmi da Kimiya da Raya Al`adun Gargajiya, wato UNESCO, ta fitar da wani rahotonta da ya fitar da alkalumma dalla-dalla, akan matsayin kasashen duniya bisa yawan kananan yaransu da ba su zuwa makarantun Firamare, ko kuma idan suka fara karatun Firamare din ba su kammalawa.
   A cikin rahoton, da Darakta Janar na UNESCO din, Mista Irina Bokoba, ya bayyana cewa kasar nan ita ce kan gaba a cikin kasashe duniya 12, da ta fi kowace kasa kananan yaran da ba su zuwa, koma ba su kammala ilmin Firamare ba, inda ya lissafta cewa a kasar nan akwai kananan yara sama da miliyan 10, wanda shine kashi 47 cikin 100, na yawan kananan yara da ba su zuwa makarantun Firamare a duniya baki daya. Sauran kasashen da yawan yaransu su ne Pakistan miliyan 5.1, sai Habasha mai yara miliyan 2.4, da Indiya mai yara miliyan 2.3, kasar Filinis da keda kananan yara miliyan 1.5.
    Sauran kasashen duniyar da suke koma baya a duniya wajen shigar kananan yaransu ko kammala ilmin Firamare sun hada da Koddebuwa mai miliyan 1.2, kasashe irinsu  Burkina Faso da Janhuriyar Nijar da Kenya kowaccensu nada kananan yara miliyan dai-daya da ba su zuwa makarantun Firamare. kasashe irin su Yamel  da Mali da Afirka ta Kudu suna da kananan yara dubu dari 9, da dubu dari 8, da dubu dari 7, bi da bi.
   Darakta Janar na UNESCO din, a cikin rahoton nasa ya ce wannan ba karamar annoba ba ce a cikin yunkurin da ake yi a duniya na ganin an kyautata fannin samar da ilmi, wanda ya ce shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa kuma ta kowane fanni, don haka yake rokon kasashen duniya da suke bayar da tallafi don tafiyar da ilmin Firamare da cewa yanzu ba lokacin su rage ko su janye tallafin da suke bayarwa ba ne, don a fadarsa, a shekarar 2011, a kalla kasashe shidda, wadanda suka hada da Kanada da Nezalan da shi kansa Bankin Duniya sun rage tallafin da suke bayarwa akan wannan fanni, ya kara da cewa kasar Birtaniya ce kadai ba ta ja da baya ba.
    Ita kanta Ministar Ilmi Farfesa Rukayyatu Ahmed Rufa`i, a wani sakon fatan alheri  da ta aika a taron kara wa juna sani akan ilmi da sashen ilmi na Jam`ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya shirya kwanan baya, ta bayyana damuwarta akan irin yadda ake da yara kanana miliyan 30, da ba su zuwa ko ba su kammala makarantun Firamare a kasashen Nahiyar, al`amarin da ta ce ko kusa ba ya taimaka wa shirin Ilmin Bai-daya. Dadin dadawa, in ji Ministar, kasashen dai Nahiyar Afirkan suke koma baya akan yawan adadin yaran da kan samu shiga makarantun Sakandare, adadin da ta ce bai wuce kashi 28, cikin 100, inda kuma za ka tarar da cewa daga dan wancan adadi da suka shiga makarantun Sakandaren, kashi 90 cikin 100,  dinsu ba sa gama karatun Sakandaren, wadanda kuma irin su ne kan kama aikin ofis, ko makancinsa da mafi kankantar albashi.
      Akwanakin baya an bayar da kiddigar dake nuni da cewa daga cikin wancan adadin kananan yara sama da miliyan 10.5, da ba su zuwa makarantun Firamare a kasar nan kusan miliyan 4.5, suna halartar makarantun allo ne, kuma suna cikin shiyyar Arewa maso Yamma, shiyyar da ta kunshi jihohin Katsina da Kano da Kaduna da Sakkwato da Jigawa da Kabbi da Zamfara. Sauran shiyyoyin Arewan wato Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas, suma suna da nasu kason kananan yaran masu halartar makarantun allon da sam-sam bas u karatun Boko. A takaicen takaitawa dai ka iya ce Arewa ita ke da kashi 70 ko abin da ya zarta hakan cikin 100, na kananan yaran da suka kamata su je makarantun Firamare, amma ba su zuwa, suna halartar makarantun Allo.
    A shiyoyin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, suna fama da matsalalolin matasan da ba su kammala karatunsu, amma su za ka taras a lokacin da suka kammala na Firamare ne suka wuce na Sakandare, sukan kauce su shiga harkokiin neman kudi gadan-gadan (kowa ya san `Yan kabilar Ibo sun yi fice akan haka). A wadannan shiyoyi biyu akasarin `ya`ya mata su iyayensu suka fi mayar da hankali wajen yin karatu tukuru, sabanin mu nan  Arewa da ba karatun `ya`ya mazan bare na `ya`ya mata da har gobe wasu suke ganin da zarar `ya mace ta yi ilmi mai zurfi wai bazata yi biyayyar zaman aure ba, don haka ga irin wadancan mutane babu bukatar ba `ya mace ilmi mai zurfi
    Mahutanta da Hukumomin ciki da wajen kasar nan da suke ta kururuwar koma bayan ilmin boko  a kasar nan, kowa ya sani cewa da mutanen Arewaci suke, inda nan ne har gobe ake kyamar karatun boko, ake kuma rige-rigen tura kananan yara makarantun Allo. Babu wani laifi iyaye su tura `ya`yansu makarantun Allo, amma inda laifin yake har ga Allah, shi ne irin kankantar yaran da suke turawa da irin kaskancin rashin abinci da suttura da wurin kwana mai kyau da barace-barace da ake barin almajiran suna fama da yi, abubuwan da suke tozarta musulmin Arewa.
    Ina ganin lokaci ya yi da gwamnatocin jihohin Arewa za su fara gina Makarantun Allo a kowane lungu da sakon jihohinsu, kamar yadda suke gina Makarantun Firamare, su kuma wadatasu da Malamai da kayayyakin aiki (a zaman na jeka-ka-dawo), a kuma rika hada karantarsu da na ilmin zamani. Ai gwamnatin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a shekarar 2009, ta fara bude irin wadannan makarantu a zaman gwaji a Sakkwato, da alkawarin za ta ci gaba da wannan aiki don ya game dukkan jihohin Arewa. Su kuma iyaye ya kamata su san cewa Annabi Ya kaura, idan suna takama da cewa karatun Allo suka yi, su sani yanzu cewa abubuwa sun canja matuka ta fannoni da dama