Karatun ’yan mata a makarantu: Iyaye a yi hattara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon mun kawo muku mukalar da AbuMaryam AbdulRahman ya yi a kan iyayen da suke dora nauyi a kan ’ya’yansu mata da suke karatu a makarantun gaba da sakandare, ko kuma suke hidimar kasa. Muna fata za ku karanta don fa’idantuwa da darussan da […]

Karatun ’yan mata a makarantu: Iyaye a yi hattara
Karatun ’yan mata a makarantu: Iyaye a yi hattara

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon mun kawo muku mukalar da AbuMaryam AbdulRahman ya yi a kan iyayen da suke dora nauyi a kan ’ya’yansu mata da suke karatu a makarantun gaba da sakandare, ko kuma suke hidimar kasa. Muna fata za ku karanta don fa’idantuwa da darussan da ke cikinta.

Assalamu alaikum ’yan uwa barkanmu da warhaka. Kamar yadda aka sani haihuwa daga Allah take, kuma ni’ima ce idan an tarbiyyantar da ’ya’ya kamar yadda ya kamata. Amma abin dubawa shi ne, yadda wasu daga cikin iyayen kan saryar da wannan baiwar da Allah Ya ba su. Allah Yana cewa “Ya ku wadanda suka yi imani ku kare kanku da iyalanku daga wuta…..”, anya hakan muke a yau? Idan muka yi nazari za mu ga cewa da yawan iyaye suna da alamar tambaya babba a kan wannan magana.
Wani abu kuma shi ne, maganar Annabi Muhammad (SAW) da ke cewa “Dukkanku makiyaya ne, kuma kowane makiyayi abin tambaya ne ga abin da aka ba shi kiwo, iyaye abin tambaya ne a kan ’ya’yansu.” Wallahi wadannan batutuwa biyu abubuwa ne masu nauyi ga dukkan mai hankali da tunanin zai koma ya sadu da Allah ranar sakamako.
Wannan gabatarwa za ta karkata ne ga yadda wasu iyaye ke gudanar da tarbiyyar ’ya’yansu mata da suke makarantar gaba da sakandire. Budurwa na bukatar a rika bibiyar ta a kowane hali domin kada a bar ta a sake haka kawai, ta yi ta ganin cewa yanzu ta girma, hankali ya ishe ta, tana iya yin abin da ta ga dama, tun da yanzu ta shiga babbar makaranta. Irin wannan hali na wasu iyayen ta kai ma daga lokacin da ’yarsu ta shiga babbar makaranta, to suna ganin kawai tamkar ’yarsu ta fara aiki ne kawai, don haka sai wasu su kyale ta, ita ce za ta rika ci da kanta a wannan makaranta. Kai wasu iyayen ma har wani nauyin za su kara mata na ta rika ba su wani abu ko kuma ta rika daukar nauyin wasu daga cikin kannenta kanana da suke wasu makarantu.
Don Allah ina hankali a cikin irin wannan abu? Shin haka ya kamata a yi tarbiyyar wadannan ’yan mata? Da yawa wanda duk ya san yadda rayuwar babbar makaranta take a halin da kasarmu take ciki ya san cewa wuri ne na ba ni ba ni a kullum ta wajen siyan kayan karatu irin su handout da irin su uwa uba toshiyar baki da ake ba wasu daga cikin malamai da dai sauran abubuwa masu neman kudi a kullum, to ta wane hali ne ake tunanin ta ci da kanta a wannan wuri?
Za mu ci gaba in sha Allah.