Karbo bashin jihohi: Ba zan sa hannu kan abin da zai jefa al’umma cikin matsala ba – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, Shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta Tarayya. Aminiya ta samu damar kasancewa daga cikin ‘yan jaridar da suka tattaunawa da shi a ofishin kungiyar ‘yan jaridu na Kaduna a wannan makon, inda ya bayyana cewa ba zai sanya hannu a karbo bashin da zai jefa al’umma […]

Karbo bashin jihohi: Ba zan sa hannu kan abin da zai jefa al’umma cikin matsala ba – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, Shi ne Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta Tarayya. Aminiya ta samu damar kasancewa daga cikin ‘yan jaridar da suka tattaunawa da shi a ofishin kungiyar ‘yan jaridu na Kaduna a wannan makon, inda ya bayyana cewa ba zai sanya hannu a karbo bashin da zai jefa al’umma cikin matsala ba. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:

 

Aminiya: Sanata me ya kawoka sakatariyar ‘Yan Jaridu?

Shehu Sani: Ziyara ce ta ba-zata na kawo domin ganawa da shugabannin wannan kungiya tare da yi masu godiya da irin rawar da suke takawa wurin ci gaba da wayar da kan talakawa da kuma ba mu goyan baya da irin gwagwarmayar da muke a halin yanzu akan bangaren ayyukanmu ko kuma abin da muka tsaya kansa. Na kuma zo ne domin in amsa tambayoyi akan wasu abubuwa dake faruwa ko a kasa ko anan jiha.

Aminiya: Akwai maganganu da ake yi cewa wai kai ne kan gaba wajen hana Jihar Kaduna karbo bashi daga kasar waje. Me zaka ce?

A halin gaskiya maganar karbar bashi ba magana ce ta wasa ba, dan ko ga musulmi an ce daya daga cikin abubuwan da za su hana mutum zama lafiya shi ne idan ana bin sa bashi. A halin gaskiya a matsayina na shugaban kwamitin Dattawa dake da alhakin sa hannu a bada bashi ko kada a bada bashi akwai sharudda wadanda dole sai an cika su sannan muke yarda a amso bashi. Na farko shi ne nawa ne zaka amsa? Na biyu nawa ne kudin ruwan da aka sa a cikin wannan bashi da ka je ka amso? Na uku me zaka yi da kudin da zaka amsa? Na hudu shin nawa ake binka a da da kuma kake son kara amsar wani bashin? Na biyar shi ne mu tabbatar da cewa idan ka ci bashin nan ba zai shake jama’a ba, inda za su zo su kasa biyu har ya kasance an mayar da kowa bawan wannan bashi da aka ci.

Akwai bashi da gwamnatin tarayya take bukatar a sa hannu wanda ya kai dalar Amurka biliyan biyar da miliyan dari biyar. Akwai kuma bashi da jihohi fiye da 19 suke bukatar sa hannun mu domin su amsa.

Wadansu jihohin abin da suka bukata bai wuce dalar Amurka miliyan 35 ba. Wadansu miliyan 50, wadansu miliyan 150.

Toh, abinda nake son kowa ya sani shi ne idan na saka hannu aka amshe wannan bashi, ba za a ga sunan gwamna ba, ba za a ga sunan dan kwangilar da ya amshi wannan kudi ba. 

Ba za a ga sunan wani jami’in gwamnati ba, sunan Shehu Sani za a gani. Yaranmu da jikokinmu da za su zo nan da Shekara ashirin har zuwa hamsin za su ga sunan Shehu Sani ne yasa aka bada bashi da sunansu. Wannan bashi fa idan aka ci sai an yi shekara 40 zuwa 50 ne ana biya ko wane shekara. Shin bashin da za a ci a zo ana biya har bayan ranka har bayan wanda ya amshi kudin har bayan wanda suke gwamnati a yanzu.

Shin bai kamata kafin a yarda da shi a tabbatar da gaskiyar wannan abin da aka ce za a yi amfani da shi ba. Toh, duk wani wanda zai iya cewa wai ni na hana a bada bashi ya dai fadi ne kawai. Eh, na hana dan sai na tabbatar da abinda za a yi da wadannan kudi, na tabbatar da inda za a biya wannan kudi, na tabbatar kuma da cewa amsar wannan kudi ba zai saka jama’a cikin ukuba da bala’i ba. Saboda haka dole sai na tabbatar da wadannan abubuwa kuma zai dauki lokaci idan na tabbatar.

Idan na tabbatar da cewa ba zai zamawa mutane matsala ba, kuma akwai ayyuka da gaske da za a yi toh, zan gayawa majalisa domin ita ce zata ce ta yarda ko ba ta yarda ba. Idan kuma na ga cewa wannan abu zai wa jama’a illa zan gayawa majalisa ita ce za ta ce za a yi ko ba za a yi ba. Saboda haka magana ta siyasa inda za a dauki yara a ba su dubu goma ko biyar su hau kan titi ba su san abin da suke jawo wa kansu ba ne. A dukka mutanen da aka sa suka yi zanga-zanga akan titi babu wanda zai samu dalar Amurka daya a cikin wannan kudi. Babu wanda zai ga wannan kudi babu wanda za a saka sunansa a cikin wadanda suka amfana da wannan kudi.

Saboda haka ba na son idan aka tafi aka yi min wanka aka sakani cikin kabarina aka rufe ni a rika cewa ga wanda ya ciwo mana bashin da muka kasa biya. Duk mutumin dake cikin gwamnati har ya shekara 40 ya san cewa idan ya kara shekara 50 a duniya ya tashi aiki. Wannan bashin za a shekara 40 zuwa 50 ana biya dole ne in tabbatar da cewa shin an ce fa wanda ya ci bashi ya mutu ba zai samu kwanciyar hankali a kabarinsa ba, sai an tabbatar da cewa an biya masa bashin dake kansa. Na shi kadai fa kenan ballantana a ce Shehu Sani na amsowa mutane miliyan bakwai bashi da aka kasa biya yanzu yaya za a kenan. Dan haka su bari inji da nawa na kaina tukunna in dai har zan ci maka bashi dole ne in tabbatar da cewa abin da zan sakawa hannu zai amfane ka.

Aminiya: Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC sun yi zama akan wannan bashi da za a karba sun kuma amince da a karbo domin za a yi wasu ayyuka da su ciki har da gyaran makarantu. Hakan ba zai sa ka amince a bada bashin ba?

Shehu Sani: Eh, magana daban kuma aiki daban. Ba zan boye maka ba ‘yan majalisun jihar nan sun je sun same ni a Abuja sun zo cikin mutunci da ladabi sun kuma bukaci goyan baya. Babu yadda za a yi abin da suka bukata kuma bada goyan baya a ce ba za a yi ba. Saboda sun ba mu girmanmu tare da nuna cewa muna da mutunci. Kuma wallahi saboda arbarkacin ‘yan majalisar jihar Kaduna duk wani abu da zamu yi domin a taimaki jihar Kaduna zamu yi shi. Mun ajiye wannan yarjejeniya sai ga shi daga baya wasu da suke cikin gwamnatin jihar da ba su son a zauna lafiya sun kuma suna ba tsirarun mata naira dari uku zuwa hudu domin su fito su yi mana zanga-zanga domin ci mana mutunci.

Su kuma tara ‘yan jaridu a ci mana mutunci, ka ga gwamnati ta rabu kashi biyu. Akwai ‘yan a zauna lafiya da suka zo suka same mu wanda mun yarda zamu ba su abinda suke so. Sannan akwai wadanda suke ganin idan aka zauna lafiya za su rasa abinda suke samu. Saboda haka su kuma ba zasu cimma burinsu na siyasa ba saboda haka sai suka koma suka sake kunna wuta tare da lalata wannan abu da ‘yan majalisu suka yi.

Ina tabbatar maka da cewa shugaban majalisar Kaduna ne tare da sauran ‘yan majalisarsa suka zo suka same mu a matsayinmu na sanatoci daga jihar Kaduna. Maganar nan har ya kusa kawowa karshe amma ga dukkan alamu gwamnatin kashi biyu ne akwai ‘yan neman a tada hankali da kuma ‘yan son a zauna lafiya. Toh, shi wanda ke shugabantar gwamnatin shi ya fi dacewa ya zabi wanda ya fi zama masa alheri. Ko yabi wadanda kullum za su rika kunna masa wuta su na hada shi rikici da jama’a suna kara masa makiya, ko kuma ya bi wadanda suke neman masa maslaha a zauna lafiya domin ya samu abinda yake so. Wannan zabi ne a gare shi. Amma ni da kake gani na idan ka zo da sulhu zan yi sulhu da kai idan kuma ka zo da yaki zan yake ka. Duk guda biyu a shirye nake.

Aminiya: Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohi tara masu neman bashinsu da kuke tantance takardunsu, ko zaka fada mana a lamba ta nawa jihar take?

Shehu Sani: Ba lamba ne ake rubutawa ba, domin zan tabbatar maka cewa akwai jihar da suka bukaci dalar Amurka miliyan 35, kamar Jigawa, akwai Katsina da suka bukaci dalar Amurka miliyan 110.

Jihar Kaduna da Ogun ne suka bukaci kudade masu yawa, inda iya Ogun ta nemi dalar Amurka 150. Abinda nake son nuna maka shi ne  a halin yanzu Kaduna ana binta bashin dalar Amurka miliyan 250. Idan ka kara miliyan 350 da yanzu take nema ya zama ana binta Dalar Amurka ýmiliyan 600 fa kenan.

Wannan bashin ba za a iya biyan shi kafin zabe mai zuwa ba. Ba kuma za a iya biyansa a zabe na can gaba ba, abu ne na shekara 40 zuwa 50 masu zuwa. Kuma dole ne mu tabbatar da cewa idan za a biya wannan kudi ba zai yi illa ga albashi da ake biya ba da kuma sauran ayyuka da ake son yi ba. Sannan ba zai yiwu mu býaka bashi ka yi ayyuka a yaba maka, amma wanda zai so ya gajeka shi kuma ya fada cikin masifa da bala’i ba. Duk wadannan abubuwa na daga cikin abubuwan da muke dubawa.

A yanzu haka akwai jihohi kusan tara ciki har da na Jihar Kaduna da za a iya dubawa. Amma a duk cikin jihohin tara babu wanda aka dauki tsageranci da tashin hankali da ci wa ‘yan majalisa mutunci da ya wuce wannan jihar. Amma ba zan boye maka ba, ‘yan majalisar jihar Kaduna sun ba mu girmanmu dan saboda su wannan abun da an rigaya an same shi. Amma akwai alamu cewa akwai wadanda ke cikin gwamnatin nan da ba sa son wannan abu ya kawo karshe. 

Aminiya: Jihar Kaduna za ta samu wannaný bashi?

Shehu Sani: Ya danganta da abin da ‘yan majalisar Dattawa dari da tara suka ce.