‘Kare da Jaki’
Assalamu alaikum Manyan gobe, yaya hutu? Tare da fatan ba a takura wa iyaye a wannan lokaci na hutu. A yau na kawo muku labarin ‘Kare da Jaki’. Labarin ya yi nuni ga kada mutum ya kai kansa inda Allah bai kai sa ba. A sha karatu lafiya. Akwai wani mai sana’ar wankin mota yana […]
Assalamu alaikum Manyan gobe, yaya hutu? Tare da fatan ba a takura wa iyaye a wannan lokaci na hutu. A yau na kawo muku labarin ‘Kare da Jaki’. Labarin ya yi nuni ga kada mutum ya kai kansa inda Allah bai kai sa ba. A sha karatu lafiya.
Akwai wani mai sana’ar wankin mota yana da Kare da Jaki. Idan dare ya yi Karen ya kasance mai tsare gidansa. Sannan idan aiki ya taso kuma jakin ne yake taimakawa.
Ran nan sai barayi suka shiga gidan mutumin kare na hango su, ya bi su da haushi har sai da suka gudu. Kowa yana ta yaba Karen sosai har sai da abin ya batawa jaki rai. Jaki ya dau alkawarin cewa shi ma wata rana za a ga ranarsa.
Bayan kwana biyu sai barayi suka sake shiga gidan mutumin jaki na kallonsu bai ce komai ba. barayin na ganin Karen sai suka hakura suka koma. Jaki na ganin za su koma sai ya shiga ihu. Mai jaki na farkawa saboda haushi sai ya shiga jibgar jaki da bulala saboda ya hana shi barci cikin dare.
Da gari ya waye sai kare ya shiga yi wa jaki dariya yana fadin ka daina kai kanka matsayin da Allah Bai kai ka ba.
Nan Jaki ya sake shiga yanayin fushi da niyyar lalubo hanyar da zai rama wulakancin da aka yi masa.