‘Kare da Saniya’
Akwai wata saniya da kare a wata gona. An dauki karen aiki a gonan ne domin ya kula da ababen gona da sauransu. Shi ko kare sai ya dau abin yana gadara wa sauran dabbobin gonar. Ranar nan wata saniya ta je cin harawa sai ta ga kare ya yi kememe a kan harawar. Sai […]
Akwai wata saniya da kare a wata gona. An dauki karen aiki a gonan ne domin ya kula da ababen gona da sauransu. Shi ko kare sai ya dau abin yana gadara wa sauran dabbobin gonar.
Ranar nan wata saniya ta je cin harawa sai ta ga kare ya yi kememe a kan harawar. Sai ta ce “don Allah ka matsa ina jin yunwa”. Sai kare ya ce “lallai ma! Rashin kunya za ki min ne? Gaskiya ina hutawa ki dawo an jima”. Abin ya yi matukar bata wa saniyar rai ga yunwa ta matsa mata.
Sai ta je ta kai kara wajen sauran shanu ’yan uwanta. Shanun suna zuwa sai suka ce da kare “ don Allah ka matsa wa saniya tana jin yunwa ta ci harawa”. Kare ya ce “tab! Wato ku ne marasa kunya ko? Ba inda zani”.  kare ya karye ya fara ihu.
Tsabagen taurin kansa da kuntatawa dabbobin gonan ba wanda ya zo taimakonsa. Saniya ko ta sunkuya ta ci harawarta.
Tare da fatan Manyan Gobe za a dau darasi kuma ba za a zama masu taurin kai ba. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi