Kare mai aikin kwashe shara

Hotunan wani kare mai tsince shara a gabar kogin Zengcuoan da ke diamen, a kudu maso gabashin kasar Sin da ke lardin Fujian, wanda ya bazu a shafukan sada zumunta na intanet. Dubban masu mu’amala da shafukan suka yi ta yaba wa wannnan kare kan yadda yake kare muhalli. Wannan kare dan shekara takwas, mai […]

Kare mai aikin kwashe shara

Hotunan wani kare mai tsince shara a gabar kogin Zengcuoan da ke diamen, a kudu maso gabashin kasar Sin da ke lardin Fujian, wanda ya bazu a shafukan sada zumunta na intanet. Dubban masu mu’amala da shafukan suka yi ta yaba wa wannnan kare kan yadda yake kare muhalli.

Wannan kare dan shekara takwas, mai lakabin “Lao Hu” da ya ga an yarda shara sai ya tattara ya kwashe daga gabar teku ya kai wurin zubarwa. Mai Karen Shen den ya ce shekara biyar ya yi yana bai wa karensa horo.

A hotunan Lao Hu da aka baza yana kai-kawo a gabar teku., inda yake kwashe shaharar da ta hada da kwalaben lemu da takalman sandal da yake tsmaowa daga ruwa.

Wani mai sharhi a shafin sadarwar intanet na kasar Sin Weibo, cewa ya yi, ‘ya kamatamutane su yi nazarin abin da wannan Karen ke aiwatarwa, don haka mu daina zubar da shahara,” a cewar @dingking