Kare mai hadama

Barkanmu  da warhaka Manyan gobe.  Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kare mai hadama’. Labarin ya kunshi yadda son kai da hadama, ya yi sanadin mutuwar kare. A sha karatu lafiya. Taku: Lubabatu I. Garba Akwai wani manomi, yana da kare da zomo. A kullum idan manomin zai je gona sai […]

Kare mai hadama

Kare mai hadama

Barkanmu  da warhaka Manyan gobe.  Da fatan kuna lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Kare mai hadama’. Labarin ya kunshi yadda son kai da hadama, ya yi sanadin mutuwar kare. A sha karatu lafiya.

Taku: Lubabatu I. Garba

Akwai wani manomi, yana da kare da zomo. A kullum idan manomin zai je gona sai zomonsa ya raka shi zuwa gona. Shi kare kuwa sai dai ya zauna a gidan ya yi ta tsokanar masu wucewa.

Rannan aiki ya yi wa zomo da manomi yawa a gona don haka sai ba su samu dawowa gida da wuri ba.

Sai can dare, duk sun dawo suna jin yunwa. Manomi ya shiga gida. Sai, kare ya zaune a kan salak din da aka ajiye wa zomo. Sai zomo ya ce da shi ya matsa masa domin ya samu ya ci abinci, amma kare ya ki.

A ranar haka zomon ya kwana ba tare da ya ci abinci ba.

Washe gari, suka koma gona da manomi. Aka sake ajiyewa zomo abincinsa irin na rannan , ashe a cikin ciyayin akwai maciji.

Da kare ya ga lokacin dawowar manomi ya kusa, sai ya yi maza ya je ya zauna a kan ciyayin da aka ajiye wa zomo. Hawansa ke da wuya sai maciji ya rika  saransa, ba iyaka a jikinsa. Ga shi kuma manomi ba ya nan. Har karen ya mutu.