Kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza ya zama wajibi — MDD

Wannan furuci na MDD da martani ne ga Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza ya zama wajibi — MDD

Gawar wani Bafalasdine da Isra’ila ta kashe a Gaza

Shugaban Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira, Philippe Lazzarini, ya ce kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza dole ne ba zabi ba.

Kalaman babban jami’in dai martani ne ga Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda a ranar Litinin ya yi watsi da kiraye-kirayen tsgaita wuta tsakaninsa da Hamas a Zirin Gaza, kungiyar da ya sha alwashin ganin bayanta.

A cikin yankin na Gaza dai, kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta ce hare-haren Isra’ila ta sama da kasa a kusa da babban asibitin al-Quds, sun jefa jami’an lafiya gami da dubban Falasdinawa da ke gudun hijira cikin firgici.

Wannan na zuwa ne a yayin da ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta sanar da karuwar adadin Falasdinawan suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila zuwa mutane sama da dubu 8,300, cikinsu kuma har da kananan yara fiye da 3,450.

Tuni dai jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci Kwamitin Tsaro ya sake yunkurawa wajen ganin an tsagaita wuta a Zirin Gaza, a daidai lokacin da hukumar UNICEF ta yi gargadin cewa kananan yara sama da 450 ake kashewa ko kuma suke jikkata duk rana a yankin.

Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu

An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina

NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini

Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji