Kare Rocko dan shekara 2 ya zama dogon karnukan duniya
Kare Rocko gaggausa ne kakkarfa, kuma yana da tsawon kafa bakwai (7ft), inda a halin yanzu ake sa ran kundin nazarin shahararrun al’marun duniya na Guinness world Record ya sa shi a jerin wadanda za a tantance, don tabbatar masa da wannamn kambi.Karen dan shekara biyu bai daina yin tsawoi ba, kuma yana ci gaba […]
Kare Rocko gaggausa ne kakkarfa, kuma yana da tsawon kafa bakwai (7ft), inda a halin yanzu ake sa ran kundin nazarin shahararrun al’marun duniya na Guinness world Record ya sa shi a jerin wadanda za a tantance, don tabbatar masa da wannamn kambi.
Karen dan shekara biyu bai daina yin tsawoi ba, kuma yana ci gaba da kiwo, inda yake cinye a kalla kofi takwas na abincin karnuka a kowace rana, tare da sauran kayan makwalshen dabbobi, a cewar masu shi Nick Helms da Jessica Williams.
“Ba mu san dalilin sdaurin girmansa da irin wannan tsawo haka ba,” inji Williams. Duk da cewa, wadannan iyalai na zaune da katon kare mai tsawon gaske a gidan su mai dakuna biyu, ma’auratan da suka fito daga Jihar Nebada ta Amurka, sun nunsa farin cikin su ga samun kakkarfan aboki “mai zuciyar tagari da katon ciki,” a cewarsu.