Kare ya hadiye Naira dubu 64,800, an biya Naira dubu 52,650 wajen ciro kudin a asibiti

Wani kare da mamallakinsa ya rada wa suna Ozzie ya hadiye tsabar kudin da aka nade a cikin takardar ambulan da ya kai Fam £160 (daidai da Naira dubu 64 da dari 8). Mamallakin karen da matarsa sun dauki nauyin ciro kudin daga cikin karen, kuma aikin ciro kudin da karen ya hadiye zai lakume […]

Kare ya hadiye Naira dubu 64,800, an biya Naira dubu 52,650 wajen ciro kudin a asibiti

Wani kare da mamallakinsa ya rada wa suna Ozzie ya hadiye tsabar kudin da aka nade a cikin takardar ambulan da ya kai Fam £160 (daidai da Naira dubu 64 da dari 8).

Mamallakin karen da matarsa sun dauki nauyin ciro kudin daga cikin karen, kuma aikin ciro kudin da karen ya hadiye zai lakume kimanin kudi Fam £130 daidai da Naira dubu 52 da dari 6 da 50 (52,650) .

Karen Ozzie, mai shekaru 9 ya hadiye kudin da ke cikin takardar ambulam din wanda aka saka a cikin akwatin sakonni na gidan su Judith da Wright da ke birnin Llandudno, a shiyyar North Wales a Ingila. Ma’auratan sun dauki karen ne zuwa asibitin dabbobi don a ciro masu kudin da karen ya hadiye ko kuma karen ya amayar da kudin. Asibitin sun sanar masu da cewa, ciro kudin daga cikin karen za su biya kudin aiki da ya kai Fan £130 daidai da Naira dubu 52 da dari 6 da 50 (52,650).

Judith ta ce, “Akwai wani da suke bi bashi kudin da yazo biya sai ya zuba kudin a cikin akwatin sakonnin gidan, hakan kare ya samu damar bude akwatin ya hadiye kudin”. Wata kakakin cibiyar asibitin dabbobi ta Murphy & Co a garin Llandudno inda aka kai karen don ciro kudin ta fada wa wanda ya mallaki karen cewa, har sai an biya kudi Naira 52,650 kafin a tilastawa karen ya amayar da kudin da ya hadiye.

Kakakin cibiyar asibitin dabbobin ta ce, wannan shi ne karo na farko da aka taba kawo masu wani kare ya hadiyi kudi. Sun fi samun a kawo masu kare ya hadiyi wani abu da ake ajiye wa a bandaki ko kuma safa. Irin wadannan karnukan su kan jefar da jakar kudi ko kuma abin daure kudi.

Mista Wright ya ce, idan aka hada kudin da karen hadiye da kudin da wanda aka kashe wajen ganin likitan dabbobi zai kai kusan Fam £300, daidai Naira dubu N121,500 duk a cikin aljuhunsu.

Mista Wright, ya kara da cewa, za su iya gano wasu kudaden ne idan aka kai su bankin Ingila. A yanzu suna shirin sanya kejin da zai zagaye akwatin sakonni, don dakatar da karen gidan daga samun damar hadiyan wani abu da aka ajiye a cikin akwatin nan gaba.