Kare ya kai kansa asibitin dabbobi bayan ya yi rauni
Karen ya kai kansa asibitin dabbobi na Cape of Good da ke Afirka ta Kudu.
Kare dabba ne da yake da juriya musamman wajen biyan bukata. Wannan ya tabbata ga wani kare mai suna Rio.
Karen mai launin baki ya kai kansa asibitin dabbobi na Cape of Good Hope SPCA, a Afirka ta Kudu ba tare da rakiya ba a ranar Juma’ar da ta gabata. Rio dai ya samu raunuka ne a wuyansa kuma yana bukatar taimako.
- Wadanda suka yi garkuwa da dan basarake a Taraba na neman N120m
- Zuriyar Dantata: Zuriyar da ta fi dukiya a Afirka ta Yamma
A cewar shafin Intanet na SPCA, karen ya tafi asibitin dabbobin, inda Shugaban Asibitin SPCA, Moyo Ndukwana ya kawo magunguna tare da tsare shi.
Ma’aikatan kiwon lafiya sun zo da sauri don duba da raunukansa tare da yi masa maganin riga-kafi, inda daga bisani ya warke. Abin bakin ciki shi ne, babu wanda ya zo neman karen kuma ba a sa masa na’urar fasahar ‘microchip’, don nuna masa hanya, kamar yadda rahoton SPCA ya ruwaito.
Akwai azurfa a jikin wuyansa, duk da haka, bayan ya wuce matakin gwajin lafiyarsa da halayensa, Rio zai shiga sashin riko na SPCA inda dangi ko mamallakinsa za su same shi su kai shi gida.
Amma ta yaya ya gane hanyar zuwa ga likitan dabbobi? Akwai dalilin faruwar hakan, a cewar Jenna Stregowski, jami’ar RBT ta Daily Paws Pet Health kuma Editar Halaye, wadda ta ce, zai iya zama “hadari ne ya faru da shi” wanda ya sa Rio ya ji rauni a yankin kuma yana neman mutane su taimaka masa.
Ya kasance yana kusa da mutane a da, don haka akwai yiwuwar ya ji kanshi da sauti na asibitin kula da dabbobi kuma ya san hanyar zuwa wurin don neman taimako.
Ta ce bayan haka karnuka suna da kwarewa sosai wajen sa-ido da leken asiri.
“Lokacin da na yi aiki a asibitocin dabbobi, wasu lokuta muna samun tsintattun dabbobin da ba su da gida a kusa- musamman karnuka,” inji Stregowski.
“Koyaushe muna tunanin cewa, suna saurin jin kanshi da sauti na likitan dabbobi. Yawancin karnuka suna son zuwa wurin likitan dabbobi, saboda suna danganta shi da mai kula, don haka watakila wannan shi ne kwarewar Rio ta baya,” inji ta.
Shafin SPCA ya ce, yana tattara rahotanni kusan 100 na dabbobin da ake kiwo a gida da suke bacewa a kowane wata, “Don haka wannan ya zama wani abin tunatarwa don sanya na’urar ‘microchip’ ga dabbarku don gano inda take,” inji shafin.