Kare ya kashe dalibin makarantar rainon yara a Fatakwal

Wani kare ya yi ajalin wani karamin yaro mai suna Dabid Emmanuel, dalibi a makarantar rainon yara ta garin Rumuagba a Karamar Hukumar Obio/Akpor, a Jihar Ribas kuma ya ji wa wani yaro mai suna Benita Adejoh rauni. Aminiya ta samu labarin cewa mai karen ya yi bulaguro zuwa kasar waje ne ya bar karen […]

Kare ya kashe dalibin makarantar rainon yara a Fatakwal
Kare ya kashe dalibin makarantar rainon yara a Fatakwal

Wani kare ya yi ajalin wani karamin yaro mai suna Dabid Emmanuel, dalibi a makarantar rainon yara ta garin Rumuagba a Karamar Hukumar Obio/Akpor, a Jihar Ribas kuma ya ji wa wani yaro mai suna Benita Adejoh rauni.

Aminiya ta samu labarin cewa mai karen ya yi bulaguro zuwa kasar waje ne ya bar karen wurin maigadin gidansa don kula da gidan da kuma karen.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa, maigadin ya bar kofar gidanne a bude sai karen ya fito da gudu bai tsaya ko’ina ba sai cikin makarantar rainon yaran da ke daura da gidan. Majiyar ta ce ganin abin da ya faru sai makwabtan makarantar suka far wa karen da jifa da duwatsu da duka da sanduna har sai da suka kashe karen.

Emmanuel ya rasu ne bayan an kai shi asibiti tare da daya yaron, daga bisani ’yan sanda sun je makarantar su tafi da shugabanta.

Shi kuma Benita Adejo ana yi masa jinyar  raunukan cizon da karen ya yi masa.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Nnamdi Omoni game da lamarin inda ya tabbatar da faruwar hakan ya ce, an kama shugaban malaman makarantar yana hannunsu domin yi musu bayani.

 

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno