Kare ya yi jana’izar dan uwansa
Wani kare ya zubar da hawaye tare da yin jana’izar dan uwansa da ya mutu abayan mota ta buge shi. Tarihi na nuna cewa, shakuwar abokantaka ta dan Adam da kare tana iya zama irin na jinsin halittar dabbobi biyu. Kare dai wani lokaci yakan shaku sosai da dan Adam kuma ya rika yin abin […]
Wani kare ya zubar da hawaye tare da yin jana’izar dan uwansa da ya mutu abayan mota ta buge shi.
Tarihi na nuna cewa, shakuwar abokantaka ta dan Adam da kare tana iya zama irin na jinsin halittar dabbobi biyu. Kare dai wani lokaci yakan shaku sosai da dan Adam kuma ya rika yin abin da mutum ke da muradi.
Kare yana kulla abota da kare dan uwansa.
A nan wani bakin kare ne ke zubar da hawaye lokacin da abokinsa kare mai farin jiki ya mutu, alamar yana nuna bakin karen bai son mutuwar abokinsa ba, bayan ya fahimci lallai ya mutu ne sai ya fusata ya fara zubar da hawaye kamar zai dauke shi.
Bakin karen ya yi yunkurin ya ceto rayuwar abokinsa.