Kareena Kapoor ta ji rauni a Dubai
Jaruma Kareena Kapoor ta ji rauni lokacin da ta je bikin bude kasuwar kayan kwalliya a Dubai makon jiya.Jarumar ta halarci bikin ne tare da Satyagraha da kuma jarumi Ajay Debgan inda masoya suka yi kukan kura don su ga jarumar, turmutsutsun ne ya sanya ta bugu a hannunta.Bayyanar jaruman wurin bikin ne ta jawo […]

Jaruma Kareena Kapoor ta ji rauni lokacin da ta je bikin bude kasuwar kayan kwalliya a Dubai makon jiya.
Jarumar ta halarci bikin ne tare da Satyagraha da kuma jarumi Ajay Debgan inda masoya suka yi kukan kura don su ga jarumar, turmutsutsun ne ya sanya ta bugu a hannunta.
Bayyanar jaruman wurin bikin ne ta jawo turmutsutsun masoyansu wanda hakan ya jawo cunkuson ababen hawa.
Da kyar aka shiga da su, wanda Satyagraha da Ajay ma ba su samu wajen zama ba sai da kyar masu daukar hoto sojoji suka samar masu wani wuri suka tsaya.
Daga karshe ne ‘yan sanda suka kawo wa jaruman dauki, sannan suka raka su suka shiga motocinsu, a nan ma masoya sun yi turmutsutsun ganin jaruman.
Sai dai har yanz
u jaruman ba su ce komai dangane da abin da ya faru ba.