Karen da ya ceci sojoji a wurin yaki ya yi ritaya daga aiki
Wani karen da ke aiki da sojoji mai suna Kuno da ya ratsa cikin harbin harsasai da abokan gaba don ya ceto sojojin Birtaniya da ke yaki da Al’Qa’ida a Afghanistan ya samu lambar yabo ta Gicciyen Victoria Cross. A yayin wani hari, karen ya kai wa wani dan bindiga farmaki, inda aka harbe shi […]
Wani karen da ke aiki da sojoji mai suna Kuno da ya ratsa cikin harbin harsasai da abokan gaba don ya ceto sojojin Birtaniya da ke yaki da Al’Qa’ida a Afghanistan ya samu lambar yabo ta Gicciyen Victoria Cross.
A yayin wani hari, karen ya kai wa wani dan bindiga farmaki, inda aka harbe shi a kafafuwansa biyu na baya.
- Budurwa mai shekara 14 da ke kiwon manyan macizai
- Yadda ake hada ‘Yogurt’ na gida (Home made yogurt)
Bayan rasa kafarsa daya ta baya a sanadiyyar harbin, Kuno ya zama karen sojojin Birtaniya na farko da aka saka wa kafar roba ta musamman.
Za a kuma karrama Kuno mai shekara hudu da lambar yabo ta Dickin daga Gidauniyar Dabbobi ta PDSA.
A halin yanzu an yi wa Kuno ritaya daga aiki – aikin da ya hada da gano bama-bamai da makamai da kuma kassara abokan gaba – kuma za a karrama shi a wani taro da za a gudanar ta Intanet a watan Nuwamban bana.
Tun farko an tura Kuno da mai kula da shi wani sansani ne don tallafa wa ayyukan wata runduna da ta kai wani hari cikin dare kan mayakan Al-Qa’ida a Afghanistan a bara.
Dakarun da ke tare da su sun kasa motsawa saboda yawan harbin da mayakan Al-Qa’ida ke yi mu su.
An saki Kuno don ya warware matsalar, kuma ba tare da wata-wata ba, karen ya ratsa cikin ruwan harsasan da abokan gaban ke harbawa sanye da wani tabarau mai taimaka wa gani cikin duhu.
Ya samu nasarar kayar da dan bindigar a kasa, matakin da ya kawo karshen harin.
A yayin harin ne aka harbe shi a kafafunsa biyu na baya kuma mai kula da shi ya sanya masa magani sannan ma’aikatan jinya suka kula da shi cikin helikwaftan da ya mayar da su sansaninsu. Daga baya an mayar da shi Birtaniya domin yi masa jinya.
A can ne aka gano yawan raunukan da Kuno ya samu, kuma likitocin dabbobi sun yanke wani bangare na kafarsa daya ta baya.
Bayan wannan lokacin ne aka yi masa aiki da ya hada da sake gina kafar tasa.
Cikin watanni sai aka sanya masa kafar roba ta musamman da ta maye kafar tasa ta baya da aka yanke.
Babban Shugaban Gidauniyar PDSA, Jan McLoughlin ya ce, jarumtar da Kuno ya nuna ce ta sa suka karrama shi da lambar yabo ta Dickin.
Wannan babbar lambar yabo ce da aka fara karrama dabbobi da ita tun 1943, kuma wannan ce lambar yabo da tafi girma da ake ba dabbobin da ke ayyuka a fagen yaki.
Kuno ne kare na 72 da za a karrama da lambar yabon, cikin karnuka 34 da tantabaru 32 da dawaki hudu da mage daya.
Rahoton BBC.