‘Karen daji da Tsuntsu’
Akwai wani Karen daji wanda gidansa ke kusa da rafi. Dabbobi daban-daban sukan je wajen don shan ruwa. Ga shi yana jin yunwa amma dabbobin dake zuwa rafin don shan ruwa ba irin wanda zai iya kamawa ba ne. Yana zaune sai ya hango wani mushen saniya. Nan take ya sheka a guje kuma ya […]
Akwai wani Karen daji wanda gidansa ke kusa da rafi. Dabbobi daban-daban sukan je wajen don shan ruwa. Ga shi yana jin yunwa amma dabbobin dake zuwa rafin don shan ruwa ba irin wanda zai iya kamawa ba ne. Yana zaune sai ya hango wani mushen saniya. Nan take ya sheka a guje kuma ya fara ci don kada zaki ya hana shi idan ya hango shi.
Yana cikin ci ne sai wani kashi ya makale masa a makogwaro. Ya yi kokarin ya fitar da kashin daga makogwaronsa amma abin ya gagara. Ya sake yin kokarin hadiye kashin amma abin ya gagara. Sai ya je wajen wani tsuntsun ya roke shi don ya taimaka masa ya cire masa kashin kuma in har ya cire masa ya yi alkawarin zai yi masa kyauta.
Nan take tsuntsun ya shigar da kansa cikin bakin Karen daji don ya cire masa kashin. Bayan ya cire masa ne sai ya tambaye sa alkawarin da Karen dajin ya yi masa amma sai Karen dajin ya ce ba zai ba shi komai ba, hasalima ya yi sa’a a lokacin da ya zura kansa cikin bakinsa bai hada da shi ya hadiya be. Sai tsuntsun ya rabu da shi. Abin ka da tsautsayi sai karen dajin ya sake komawa wajen mushen saniyar ya cigaba da ci can sai wani kashin ya sake makale masa a makogwaro sai kuma ya sake komawa wajen tsuntsu don ya taimaka masa ya sake cire masa, inda ya yi alkawarin ba shi kyauta. Ya ce “dama dazu ina yi maka wasa ne, amma yanzu idan ka cire mini zan cika maka alkawari. Tsuntsu da jin haka sai ya kakkabe fukafukinsa ya tashi ya bar Karen Daji yana ta kakarin mutuwa.