Karim Benzema ya lashe kambun Ballon d’Or na 2022

Benzema ya lashe kyautar kwana daya bayan da Madrid ta lallasa abokiyar adawarta, Barcelona.

Karim Benzema ya lashe kambun Ballon d’Or na 2022

Benzema

Dan wasan Real Madrid da Faransa, Karim Benzema ya lashe kambun Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya na bana.

Kyautar na zuwa ne kwana daya bayan dan wasan ya jagoranci Real Madrid wajen lallasa abokiyar adawarta, Barcelona da ci uku da daya, inda ya zura kwallo daya a minti 11 da fara wasa, sannan Madrid din ta yi dare-dare a teburin Gasar Laliga.

A bara, dan wasan kungiyar PSG da kasar Ajantina, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a karo na bakwai.

Messi ne ya fi kowa tara kambun, inda yake da bakwai, sai Cristiano Ronaldo na Manchester United da ke biye masa da guda biyar.

Rawar da Benzema ya taka

Kakar wasannin bara za ta iya kasance kakar wasanni da ta fi yi da Benzema.

Benzema ya kasance wanda za a iya cewa ya dauki nauyin Kungiyar Real Madrid a kakar bara, inda ya rika zura kwallaye a duk lokacin da kungiyar take bukata har ta kai ga samun nasarar lashe Kofin Zakarun Turai.

A ranar 9 ga Maris din bara Benzema ya zura kwallo uku rigis a minti 17 a wasan zagaye na biyu a tsakanin Real Madrid da PSG yana mai shekara 34.

Da wannan zura kwallayen ne Benzema ya kafa tarinin wanda ya fi shekaru da ya zura kwallo uku rigis a Gasar Zakarun Turai.

Bayan nan Benzema ya ci gaba da zura kwallaye a kusan duk wasan Real Madrid, inda da zarar ba ya cikin wasa, magoya bayan kungiyar sukan shiga damuwa da rashin tabbas na samun nasara.

A ranar 30 ga Afrilun bara kuma da taimakon kwallayen da Benzema ya rika zurawa Real Madrid ta lashe Gasar La Liga karo na 35, inda ya zura kwallo daya a wasan da kungiyar ta lallasa Espanyol da ci 4-0 a Filin Wasa na Bernabeu.

A Gasar Zakarun Turai kuma, a wasan farko na Kwata Fainal Real Madrid ta doke Chelsea da ci 3-1.

Da aka dawo wasa na biyu, sai Chelsea ta yi wa Madrid din shigar wuri inda ta ci kwallo 3, wanda ya jefa magoya bayan kungiyar a cikin fargaba da tsoro.

Ana cikin hakan ne Rodrigo ya farke kwallo daya, wanda hakan ke nufin kunnen doki, kafin Karim Benzema ya jefa kwallo a minti 96, inda suka yi waje da Chelsea, Madrid kuma ta tsallaka wasan dab da na karshe.

A wasan dab da na karshe, Real Madrid ta fafata da Manchester City, inda Benzema ya zura kwallo a ranar 4 ga Mayun bara daga fanareti.

Da haka ne ya yi waje da Man City din, sannan ya tsallakar da Madrid zuwa wasan karshe, inda suka doke Liverpool da ci daya mai ban haushi ta lashe kofin karo na 14.

A kakar bara, Benzema ya lashe kambun wanda ya fi zura kwallo a raga a Spain (Pichichi) da kwallo 27 a wasa 32.

Sannan ya zama wanda ya fi zura kwallo a Gasar Zakarun Turai da kwallo 15, kuma Gwarzon Dan Kwallon Gasar Zakarun Turai.

Ronaldo da Messi sun mamaye kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya

A shekarar 2007 ce dan wasan Brazil Ricardo Kaka ya lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Duniya, Messi ya zo na biyu, Ronaldo na uku.

Tun wancan shekara ba a sake samun wanda ya lashe kyautar ba bayan Ronaldo da Messi sai shekarar 2018 da Luka Modric ya samu, sai kuma na bana.

Ke nan sai da suka dauki kyautar sau 12 a tsakaninsu.

Sannan duk a wadannan shekaru, sun zura kwallaye da yawa, sun ci kofuna da dama, sannan sun karya tarihi da yawa.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50