Karin albashi: Nan gaba za mu sanar da matsayarmu kan yajin aiki —NLC

Nan gaba kungiyar kwadago za ta zauna da rassanta don daukar matsaya kan janye yajin aiki bayan gwamnati ta yi alkawarin kara mafi karancin albashi ya haura N60,000

Karin albashi: Nan gaba za mu sanar da matsayarmu kan yajin aiki —NLC

Ana kyautata zaton nan gaba kungiyar kwadago ta janye yajin aiki da ta shiga don neman karin mafi karancin albashi.

Nan gaba ake sa ran kungiyar za ta sanar da matsayar da ta dauka kan karin albashin bayan wata yarjejeniya da cimma da gwamnati a zaman da suka yi a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

A safiyar Talata kungiyar ta sanar cewa za ta zauna da rassanta ta ji daga gare su, domin daukar matsaya kan wannan lamari.

Ana kyautata zaton janye yajin aikin ne bayan gwamnati ta amince ta kara mafi karancin albashin ya haura Naira dubu sittin da ta gabatar wa kungiyar kafin zaman.

Bangarorin sun yi ittifaki kan haka ne a zaman sirrin da suka gudanar a daren Litinin da kungiyar ta fara yajin aikin gama gari a fadin Najeriya.

Bayan ganawar bangarorin suka fitar sanarwar cimma matsaya da cewa, “Shugaban kasa a shirye yake da ya kara mafi karancin albashi daga N60,000.

“Bangarorin za su ci gaba da tattaunawa a kullum na tsawon mako guda domin cimma matsaya kan wannan lamari.

“Kungiyar kwadago za ta je ta tattauna da rassanta kan wannan tayi, domin cim ma matsaya.

“Babu wani ma’aikaci da za a gallaza wa saboda shiga yajin aikin.”

Da haka ake kyautata zaton kungiyar kwadago za ta sassauta yajin aikin nata.

Yajin aikin dai ya durkusar da harkokin gwamnati da na kamfanoni da sana’o’in dogaro da kai.