Karin albashi: An yi ba a yi ba
A makon jiya ne Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara harajin kayayyaki (BAT) inda zai tashi daga kashi biyar zuwa kashi bakwai da rabi. Hajiya Zainab ta bayyana haka ne bayan taron Majalisar Zartarwa, inda ta yi nuni da cewa karin harajin zai samar da kudin da Gwamnatin […]
A makon jiya ne Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kara harajin kayayyaki (BAT) inda zai tashi daga kashi biyar zuwa kashi bakwai da rabi.
Hajiya Zainab ta bayyana haka ne bayan taron Majalisar Zartarwa, inda ta yi nuni da cewa karin harajin zai samar da kudin da Gwamnatin Tarayya za ta iya biyan albashi mafi karanci na Naira dubu 30 da ta amince da shi a watannin baya.
Haka kuma Gwamnatin Tarayya za ta taimaka wa gwamnatocin jihohi da wani bangare na kudin harajin domin su samu saukin biyan sabon albashi mafi karancin.
Wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka ya jawo cece-ku-ce a tsakanin al’immar kasar nan saboda ana ganin bai kamata gwamnati ta kara harajin kayayyaki a wannan mawuyacin halin da ake ciki ba, domin babu abin da hakan zai haifar sai kara tsadar kayayyaki.
Tun farko ba a taba karin albashi ba tare da mutane sun fuskanci matsala ba, domin farashin kayayyaki zai tashi, ta yadda karin da aka yi wa ma’aikaci ba zai amfane shi ba. Shi ya sanya ake ganin maimakon shugabannin ma’aikata su matsa wa gwamnati ta kara albashi ga ma’aikata gara su rika matsawa wajen ganin gwamnati ta samar da muhimman ababen more rayuwa, kamar wadata asibitoci da magani tare da bayar da magani kyauta da bayar da ilimi ingantacce kuma kyauta da samar da gidaje masu saukin kudi da ma’aikaci zai iya mallaka ya biya a saukake da samar da yanayin da ma’aikaci zai mallaki abin hawa ta hanya mai sauki da kuma tabbatar da ganin gwamnati ta wadata kasa da abinci yadda ma’aikaci zai iya cin abinci sau uku a rana tare da iyalinsa ba tare da matsala ba.
Idan aka samu haka babu shakka ko nawa ake biyan ma’aikaci a matsayin albashi zai yi masa auki domin an dauke masa nauyin muhimman al’amuran rayuwa. Amma yanzu da aka bar ma’aikaci yana fama da kudin makarantar yaransa da kudin magani a asibiti da kudin hanyar gida da kudin zirga-zirga zuwa wurin aiki, ta yaya albashinsa zai yi masa auki har ya kulla wani abin kirki daga ciki?
Yanzu an ce an yi karin albashi, tun kafin a fara biyan ma’aikata har farashin wasu kayayyaki ya tashi, idan kuma aka kara harajin kayayyaki dole a kara farashin kayayyakin tunda kamfanoni masu samar da kayayyakin suna bukatar samun riba ne.
Ba karuwar farashi kawai karin harajin zai haifar ba, har ma rashin aiki zai karu, domin kamfanoni da dama za su rage ma’aikatansu domin su samu sukunin biyan harajin.
Wato dai karin albashin da aka yi ya zama an yi ba a yi ba ke nan, domin maimakon karin ya zama alheri ga ma’aikaci sai ya zame masa matsala, to ina amfanin badi ba rai? Wato gwamnati ta kara wa ma’aikaci kudi da hannun dama amma ta kwace da hannun hagu, an yi wa ma’aikaci wala-wala ke nan.
Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da mawuyacin halin da jama’a suke ciki, ta yi kokarin fito da hanyoyin da mutane za su samu saukin rayuwa maimakon daukar matakan da za su kara uzzura wa jama’a.
Karin da za a yi na harajin kayayyaki domin a samu kudin da za a biya sabon tsarin albashi ba ma’aikaci kadai matsalar za ta shafa ba, har da sauran talakawa wadanda su ne suka fi yawa kuma suka fi jin jiki saboda mawuyacin halin da ake ciki.
Ba kowace shawara ce ya kamata Shugaban Kasa ya rika karba daga mashawartansa ba, domin masu iya magana suna cewa ‘ciyawar da ke cikin ruwa ba ta san ana rana ba,’ masu ba da shawarar nan ba su san talaka yana cikin wahala ba, domin labari kawai suke ji, kuma ga dukkan alamu gani suke yi ana zuzuta lamarin ne kawai, shi ya sanya suke ta kara fito da hanyoyi masu tsauri da za su kara gigita talakawa.
Bayan karin harajin kayayyaki da za a yi, ana kuma rade-radin cewa za a kara farashin man fetur, to ina talaka zai sanya kansa? Don Allah Shugaban Kasa ya fito da wata hanya da zai rika yin shigar burtu yana shiga cikin talakawa domin jin halin da suke ciki, domin dogara da rahotannin na kusa da shi kawai ba zai taba sanin ainihin halin da talakawansa ke ciki ba. Idan kuma an san cewa zai rika yin binciken wasu abubuwan da kansa tare da yin ziyarar ba-zata, to kowa zai shiga taitayinsa.
Ba Shugaban kawai ba, ya kamata gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da sauran shugabanni su rika kokarin ziyarar ba-zata tare da yin bad-da-bami domin sanin halin da jama’arsu ke ciki. Ya Allah Ka kawo mana saukin rayuwa, amin.