Karin albashi: Yadda aka yi wa ma’aikata rufa-ido
Ga dukkan alamu har yanzu za a ci gaba da tattaunawa game da batun karin albashi da Kungiyar Kwadago ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi, domin gwamnati ta amince za ta biya Naira dubu 30 ne kawai a matsayin mafi karancin albashi a fadin kasar nan. Wannan yunkuri da Gwamnatin Tarayya ta yi da farko […]
Ga dukkan alamu har yanzu za a ci gaba da tattaunawa game da batun karin albashi da Kungiyar Kwadago ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi, domin gwamnati ta amince za ta biya Naira dubu 30 ne kawai a matsayin mafi karancin albashi a fadin kasar nan.
Wannan yunkuri da Gwamnatin Tarayya ta yi da farko ya dadada wa ma’aikata rai, musamman a ranar da Shugaba Buhari ya sanya hannu a dokar da ta mayar da karancin albashi ya koma Naira dubu 30. Sai dai kuma daga baya sai murna ta koma wa ma’aikata ciki, domin sun dauka kowane ma’aikaci ne zai samu karin da aka yi, ashe karin ya shafi wadanda albashinsu bai kai Naira dubu 30 ba ne kawai. Wato maimakon kari da ake zaton an yi ashe gyaran albashi aka yi kawai, inda aka mayar da karancin albashi ya tashi daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 30.
Babu shakka kungiyar ma’aikata ta yi kuskure wajen gabatar da bukatunta ga gwamnati, domin ita ta dage ne wajen ganin an mayar da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, maimakon ta tabbatar cewa karin ya shafi kowane ma’aikaci.
Kamata ya yi ya kasance cewa tunda karin da aka yi na karancin albashi daga Naira dubu 18 zuwa Naira dubu 30 ya kai kashi arba’in, to wakilan ma’aikata a wurin tattaunawar su tabbatar kowane ma’aikaci ya samu irin wannan kari, amma sai suka yi zaton mayar da karancin albashi ya zama Naira dubu 30 kawai ya hada komai da komai, ba tare da fahimtar matsalar da suka jawo wa sauran ma’aikatan da ke karbar albashin da ya haura Naira dubu 30 ba.
Ga dukkan alamu gwamnati ta fahimci kuskuren kungiyar ma’aikata kafin ta sanya hannu a dokar, shi ya sanya bayan Shugaban Kasa ya sanya hannu sai gwamnati ta fito fili ta ce karin albashin zai shafi ma’aikata daga matakin albashi na shida zuwa kasa ne kawai, maimakon kowa da kowa.
Shi ya sanya ake so wadanda za su zama wakilan jama’a su zama zakakuran mutane wadanda idanunsu a bude suke ba za a yi musu wayo ko wala-wala ba, domin ana iya amfani da kalma daya kawai a jefa su cikin rami. Kamata ya yi don guje wa faruwar haka bayan an tattauna an kai wata matsaya kafin wakilan ma’aikata su amince sai su ce za su yi shawara, daga nan sai su kara tuntubar kwararru domin su tabbatar ba a yi musu rufa-ido ba.
Amma a wannan tattaunawar da aka yi da kungiyar ma’aikata an yi masu rufa-ido wanda ya sanya ba su fahimci kuskuren da suka yi ba har sai da aka sanya hannu a yarjejeniyar lokacin da aka zo aiwatarwa.
Irin haka ne aka yi lokacin da Shugaban Kasa Janar Sani Abacha ya kafa kwamitin da zai bayar da shawarar kason da za a rika ba yankin Neja-Delta daga kudin man da ake samu, inda kwamitin ya amince a rika ba yankin abin da bai WUCE kashi 13 ba, amma sai shugaban kwamitin, wanda dan yankin Neja-Delta ne, ya rubuta a rahoton da za su mika cewa kwamitin ya amince a bayar da abin da bai GAZA kashi 13 ba.
Wato su ’yan kwamiti sun ce abin da bai WUCE kashi 13 ba, ma’ana duk abin da za a bayar kada ya wuce kashi 13, amma a rahoton nasu aka rubuta cewa duk abin da za a bayar kada ya GAZA kashi 13, ma’ana abin da duk za a bayar zai fara ne daga kashi 13, ba kasa da haka ba, kuma sauran ’yan kwamitin ba su lura da bambancin ba, tun da sun ga kashi 13 sai kawai suka sanya hannu a haka. Shi ya sanya yanzu ake ba yankin Neja-Delta kashi 13 na kudin man da ake samu da suka samu latsi kuma sai suka matsa har sai da ’yan Majalisar Wakilai suka mayar ana hada man tudu da na teku wajen ba su kashi 13 din, maimakon na kan tudu kawai da aka amince tun farko tunda shi ne ba ya da yawa. Wakilan yankin Arewa kuma suka sanya hannu a dokar saboda rashin sanin illar da hakan zai yi wa yankinsu.
Ya kamata wannan ya zama darasi ga yankin Arewacin kasar nan yadda al’ummarta za su fahimci cewa ba kowa ne za su rika turawa ya wakilce su a majalisa ba, domin wuri ne na yin dokoki, idan suka tura wadanda iliminsu bai yi zurfi ba, haka nan za su rika amincewa ana bautar da yankinsu saboda rashin sani, domin wata kalma daya kawai za a yi amfani da ita a jefa su a rami ba su sani ba.