Karin albashin da Gwamnatin Tarayya bai wajaba a kanmu ba amma …. Gwamnoni
Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun bayyana cewa ba za su aiki da yarjejeniyar biyan mafi karancin albashi da Gwamnatin Tarayya ta cimma tare da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ba. Wani rahoto da Jaridar Premium Times (Hausa) ta wallafa ta ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Mista Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a Abuja, […]
Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun bayyana cewa ba za su aiki da yarjejeniyar biyan mafi karancin albashi da Gwamnatin Tarayya ta cimma tare da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ba.
Wani rahoto da Jaridar Premium Times (Hausa) ta wallafa ta ce Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Mista Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a Abuja, jim kadan bayan tashi daga wani taro da gwamnonin suka yi.
An gudanar da taron ne a otal din Hilton, kuma dukkan gwamnonin sun halarta.
Da yake jawabi a madadin gwamnonin, Gwamna Fayemi ya ce Gwamnatin Tarayya daban, haka kuma gwamnatocin jihohi daban.
Don haka za su koma su duba abin da zai fisshe su a kowace jiha, don tattauna adadin da za su iya kara wa ma’aikata a kan albashi.
Sai dai ya ce gwamnoni sun amince cewa mafi karancin albashi ba zai yi kasa da Naira dubu 30, ga masu matakin albashi na 1 zuwa 6, kamar yadda sabuwar doka ta gindaya ba.
Amma daga mataki na 7 zuwa na 17, ba za su iya yin karin kusan kashi 60 bisa 100 ba, sai dai su yi kintace su dan kara musu abin da ya sauwaka kawai.
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta yi karin kashi 20 cikin 100 ga masu matakin albashi na 7 zuwa 8, sai kashi 19 ga masu na 9, sai kuma kashi 16 ga masu 10 har zuwa 14.
Masu matakin albashi na 15 zuwa 17 ne aka amince za a yi wa karin kashi 14 cikin 100.