Karin alhazan Kwara 2 sun rasu a Makkah
Rasuwar Alhaji Salman Muhammad Alade da Hajiya Ayishat Shuaib Ologele, ya kai adadin maniyyantan Kwara da suka rasu a Hajjin bana zuwa hudu.
Karin maniyyatan Najeriya biyu daga Jihar Kwara sun rasu a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Rasuwar Alhaji Salman Muhammad Alade da Hajiya Ayishat Shuaib Ologele, ya kai adadin maniyyantan jihar da suka rasu a aikin Hajjin bana zuwa hudu, maza biyu, mata biyu.
HajiyAyishat Shuaib Ologele ta gamu da ajalin ne a hanyar zuwa Makkah daga Madina, a lokacin da ta fadi, amma duk da kokarin da aka yi na ceto rnata ta ce ga garinku nan.
Shi kum Alhaji Salman Muhammad Alade, ya rasu ne daga bisani a birnin Makka.
- Ma’aikata miliyan 5.3 za a kara wa albashi a Najeriya
- Wakilan Aminiya sun tsallake rijiya da baya a Kano
- An kama shi da kokon kawunan mutane takwas
Kawo yanzu dai babu sanarwa a hukumance game da musabbabin rashe-rashen biyu, amma hukumar jin dadin alhazan jihar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan alhazan.
Babban Sakataren hukumar, Abdulsalam Abdulkadir, ya tabbbatar wa wakiilnmu da rasuwar ta sakon WhatsApp, cewa, “Gaskiya ne mun yi rashin karin maniyyata biyu, za mu yi magana anjima, yanzu ina halartar taro ne.
“Muna mika jajenmu ga iyalansu da kuma rokon samun rahama a gare su”, in ji shi.
Kafin yanzu jihar Kwara ta yi rashin Alhaji Saliu Mohammed da kuma Hawawu Mohammed a kasar Saudiyya.