karin farashin kananzir
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kara farashin kananzir daga naira 50 zuwa 83 kowace lita. A farkon makon nan ne Hukumar da ke Kula kayyade Farashin Albarkatun Man Fetur (PPPRA) ta ce daga yanzu wannan ne sabon farashinsa.Kodayake, a baya da aka kayyade farashinsa a kan naira 50, ba a iya samunsa a kan […]
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kara farashin kananzir daga naira 50 zuwa 83 kowace lita. A farkon makon nan ne Hukumar da ke Kula kayyade Farashin Albarkatun Man Fetur (PPPRA) ta ce daga yanzu wannan ne sabon farashinsa.
Kodayake, a baya da aka kayyade farashinsa a kan naira 50, ba a iya samunsa a kan hakan idan ba a gidajen mai na gwamnati mallakar kamfanin NNPC ba. Ko a gidajen man NNPC din da ake sayar da shi a kan hakan za ka samu dogayen layukan jama’a wadanda suke kwashe kwana da kwanaki kafin samunsa.
karin farashin ba zai rasa nasaba da cire tallafin a kan albarkatun mai da gwamnati ta yi ba. Daga ranar 1 ga wannan watan ne, gwamnatin tarayya ta dakatar da tallafin da take ba dillalan man fetur da kuma na kananzir saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Masana suna ganin wannan karin zai jawo farashin kananzir ya yi tashin gwauron zabi a gidajen man da ba na gwamnati ba. Hakan zai haifar da damuwa ga talakawa wadanda suke ganin gwamnati za ta kara jefa su cikin wahala. Kodayake, dillalai masu zaman kansu sun ce karin farashin bai shafe su ba, saboda ba su taba samunsa a farashiin da hukuma ta kayyade ba. Daga nan sai suka ce za su sayar da shi ne bisa la’akari da farashin da suka samo shi. Hukumar kididdiga ta ce a gidajen matsakaitan ’yan Najeriya ana kashe kimanin Naira 500 wajen dafa abinci kuma rabin kudin ana kashe su ne kan kananzir.
Dalili da yadda masu matukar bukatar kananzir ba sa iya samunsa a farashin da gwamnati ta kayyade, ya sa wasu suke tafiya daji don yin itacen girki. Gawayi da itace su ne aka fi amfani da su wajen makamashi a yankunan karkara da gidajen talakawa da ke birane kuma hakan zai ci gaba bayan karin farashin kananzir. Wannan ba labari ne mai dadi ba ga masu rajin kare muhalli da kuma dazuka. Dazukan kasar sun ragu da kashi daya bisa hudu kasa da abin da Hukumar Abinci da Aikin Gona ta ce yakamata kasar nan ta mallaka.
Wata matsalar sayar da kananzir a farashi mai rahusa shi ne yadda wasu bata garin dillalansa suke sayar wa kamfanonin sufurin jiragen sama don amfani da shi a matsayin man jirgi. Shugaban kungiyar Masu Kamfanonin Jiragen Sama a kasar nan (AON) Kaftin Nogie Meggison ya bayyana a kwanakin baya cewa “dillalan kananzir suna sayar mana da shi.” Ya ce Hukumar da ke Kula da Sufurin Jiragen Sama (NCAA) ta ce tana da labarin haka saboda sun sanar da ita. Ya ce Hukumar da ke Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya ta ce ta shaida wa masu kamfanonin jiragen sama na kasashen ketare kan su yi hankali da man jirgin da suke sha a kasar nan. Wannan ya sa wasu masana suke ganin karin farashin kananzir zai iya maganin wannan matsalar.
A baya gwamnati ta taba fito da shirin amfani da risho wanda zai taimaka wajen rage yadda ake sare bishiyoyi. Kodayake, an kasa tabbatar da dorewar shirin. Bayan wannan shirin, an samar wa mazauna yankunan karkara sundukan makamashin iskar gas masu nauyin Kilogram uku da kuma biyar. An yi shirin samar da wuraren samar da isakar gas a duk fadin kasar nan don masu amfani da shi su samu a kusa da su cikin sauki. Akwai dimbin alfanu ta fuskar kiwon lafiya da muhalli da kuma tattalin arziki idan kowa zai koma amfani da isakar gas, sai dai har yanzu dimbin jama’a suna ganin amfani da iskar gas makamashi ne na masu hannu da shuni.
Ya dace gwamnati ta fito da wani shiri don wayar da kan ’yan Najeriya da ke karkara da kuma birane kan muhimmacin amfani da makamashin iskar gas, wanda ba ya gurbata muhalli kamar kananzir, ko itace. Ba gaskiya ba ne yadda yawancin ’yan Najeriya suke kallon iskar gas abu da ke da matukar tsada. Da zarar mutum ya mallaki na’urar gas dinsa wadda ake kera masu saukin farashi yanzu a kasar nan, daga nan sai ya sayi iskar gas wadda take da arha idan aka kwatantata da kananzir. Yakamata ya yi gwamnati ta yi amfani da wannan damar don ganin hakan ya tabbata.