Karin farashin lantarki ya tayar da kura a Najeriya
Idan har ba a rage ba to bai kamata a yi tunanin karawa ba
‘Yan Najeriya sun bayyana bacin rai kan karin farashin wutar lantarki da ya fara aiki a ranar Talata 1 ga Satumba, 2020.
Sun bayyana karin na kashi 50 a matsayin karin matsin lamba ga yadda suke rayuwa a daddafe bayan illar da COVID-19 ta yi wa hanyoyinsu na samu.
Masu kananan sana’o’i da masu masana’antu da masu sana’ar hannu da dangoginsu sun ce karin ya zo a lokacin da bai dace ba sannan ba a yi la’akari da halin da suka tsinci kansu ba a daidai lokacin da suke kokarin farfadowa daga asarar da kullen COVID-19 ya haddasa musu.
Sabon karin farashin ya shafi masu amfani da wutar lantarki da ke samunta na akalla awa 12 a rana da marasa mitoci da gidaje da masana’atu da sauran muhimman wurare.
Sai dai kuma ba zai shafi talakawa ba da marasa shan wuta sosai ba, wadanda za su ci gaba da biyan Naira hudu kan kowane kilowatt a awa guda.
Karin bai kuma shafi masu samun kilowatt 50 a wata ba kuma da wadanda ba sa samun ta na kasa da awa 12 a rana.
- Ana ta korafe-korafe
Sai dai wasu masu karamin karfi da wakilanmu suka tattauna da su a ranar Talata sun ce yana da wuya a bambance masu samun wutar ta kasa da awa 12 a rana.
Sun kuma ce karin zai yi illa ga kananan masana’antu ciki har da masu casr shinkafa da ke cewa zai kawo karuwar kudin da suke kashewa.
- Yadda NERC ta amince da karin
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin ne bayan rahoton kwamitin wucin gadi da ya kafa kan batun a watan Yuni.
Wani dan kwamitin ya ce sun nemi a kara kudin wutar ne domin guje wa kara lalacewar wutar, kasancewa babu abun da gwamnati ta ware domin tallafa wa bangaren a kasafin 2020.
Ya ce kara lalacewar wutar za ta yi illa da zai iya kaiwa ga durkushewar tattalin arzikin Najeriya.
“To sai mu tsaya mu bari tattalin arziki ya durkushe? Ai ba zai yiwu ba.
“Shi ya sa taron da muka yi ya dage cewa ba za a yi wa talakawa wadanda yawancinsu ke kan layin gidaje na R1 da R2 kari ba.
“Mun kuma samu tabbaci daga sama cewa karin ba zai shafi talakawa ba; kuma gwamnati ba ta rufe kofar tattaunawa ba”, inji shi.
Sanarwar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta aike wa kamfanonin wutar (Discos) ta ce ta amince da karin ne zuwa ranar 1 ga watan Janairun 2021.
Sai dai NERC ta wajabta wa Discos tattaunawa da kuma ba wa masu amfani da wutar tabbacin samun wutar ta fiye da awa 12 a kullum daga ranar 1 ga Satumba 2020.
- Yadda jama’a ke caccakar karin
Wani mai shagon aski a Rukudin Gidaje na Kado da ke Abuja, John Garba, ya koka da cewa bayan karin kudin man fetur da yake sanya wa janaretonsa, yanzu kudin lantarki ya karu da kashi hamsin a unguwar da ke samun wuta na kimanin awa 12.
“Ba za mu iya jurewa ba a wannan lokaci na COVID-19 da ba a samun ciniki sosai”, inji shi.
Bello Olagoke, mazaunin Maraba a Jihar Nasarawa, ya nun tababa kan rashin kari ga marasa samun wutar ta awa 12 a kullum.
Ya ce, “To wa zai taka wa DisCos din burki idan suka ga damar kara wa marasa samun wutar kudi?
“Ko yanzu abun da ake karba a hannunmu ya wuce misali duk da yawan dauke wutar da ake yi”.
Wani Malami a Jami’ar Jihar Legas, Dakta Isiaka Adams ya ce karin ya nuna gwamnati ba ta damu da halin da ‘yan kasa ke ciki ba.
Malamin a Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa ya ce, “bai dace ba a wannan lokaci duk da dalilai da matsin da Discos da Kamfanonin samar da wutar (Gencos) suke yi.
“Ba a sa wa ‘yan Najeriya mitoci ba amma ana neman su biya N38,800 kan mita mai layi daya a kasar da mafi karancin albashi N33,000 ne wanda yawancin jihohi da Gwamantin Tarayya ba su ma fara biya ba.
“Ga shi kuma gwamnati na matsa wa mutane da haraji iri-iri” inji malamin jami’ar.
Wan mai casar shinkafa a Kano, Saminu Ya’u Kangon Kaloma ya ce karin kudin wutar zai sa shinkafa ta kara tsada.
“Sai mutum ya yi amfani da wuta kafin ya cashe shinkafa saboda haka dole farashi ya tashi.
“Kudin buhun shinkafar da ake sayarwa N23,000 zai karu saboda dole sai mun kara farashin ‘yan sari”, inji Saminu.
Musa Malami Sakatare mazaunin unguwar Dakata a Kano ya bayyana kaduwa da karin farashin.
“Ina aikin tatsar man gyada ne kuma kodayaushe da wutar lantarki muke amfani.
“Ina ganin wannan karin zai sa sai mu ma mun yi wa kwastomominmu karin farashi”, inji dan kasuwar.
- Manayan masa’antu sun koka
Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya (MAN) ta yi watsi da karin da ya fi shafar ‘ya’yanta a matsayin kara jefa ‘yan kasa cikin matsi.
Mukaddashin Darketa-Janar na MAN Ambrose Oruche, ya ce babu hikima a karin farashin alhali masu masana’antu na kokawa da matsalar rashin samun ciniki da yawan harajin da suke biya baya ga kudin da suke kashewa wajen samar wa kansu da wutar ta hanyar amfani da janaretoci.
Ya ce sabon tsarin farashin zai yi illa ga tattalin arzinkin kasa ta fuskar raguwar kayayyakin da ake samarwa a cikin gida (GDP) da tsadar kaya da rashin ayyuka da kumar raguwar kudaden shiga na gwamnati.
“A halin da ake ciki, idan ba za a rage kudin wutar lantarki ba to bai kamata a kara ba, duba da tsananin tsada da ake fama da shi na kera kayan masana’antu”, inji shi.